Yadda wani bature ya harbe wata baƙar mace yai tunanin cewa Dorinar ruwa ce


Wani rahoto daga ƙasar Afrika ta Kudu na nuna cewa ƴan sanda sun bayyana cewa wani manomi farar fata ya harbe wata mace baƙar fata da ya ce ya yai tunanin dorinar ruwa ce, shiyasa ya harbe ta.


Paul Hendrik van Zyl mai shekaru 77 a ranar Talata da ta gabata An dai kama mutumin bayan da yayi wannan harbin a kusurwar da matar take kamun kifi a wani kogi dake garin Lephalale a yankin arewacin Limpopo tare da abokiyar kamun kifin ta.


Mutumin dai na fuskantar tuhuma ce a kan yunkurin kisan kai a cewar masu gabatar da ƙara na ƙasar, duba da cewa raunuka matar ta samu.


Mai magana da yawun ƴan sandan Mamphasa Seabi ya ce lallai, ana tunanin wanda ake zargin ya harbi matar ce a lokacin da yake zaton dorinar ruwa  ce a wurin.


Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki sosai inda wasu ke tunanin cewa Dorinar ruwa ba za ta taɓa yin kama da mutum ba, domin siffar mutum daban take da ta dabba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post