Masana Sun Tabbatar Cewa Za'ayi Azumi 30 A Najeriya Da Ƙasar Saudiyya A Bana


A cigaba da shirye-shiryen da musulmi suke yi a Najeriya na fara duban watan Shawwal a ranar Asabar domin sauke azumin watan Ramadan, sai dai kuma wani shahararren masanin ilimin Sararin samaniya Adamu Ɗan Amurka ya yi karin haske kan yadda za'a yi azumin bana guda 30 a Najeriya da ƙasar Saudiyya.


Shahararren masanin, ya bayyana hakan ne shafin sa na sada zumunta na kwamitin ganin wata dake ƙarƙashin fadar Mai alfarma sarkin musulmi ya. Inda yai iƙirarin cewa, za a samu kisfewar wata a cikin watan Shawwal cikin ikon Allah, wanda hakan ke nuna da wuya a samu ganin watan Shawwal a ranar Asabar.


Adamu ya ƙara da cewa, “Idan baku manta ba tun shekaran da ta wuce lokacin da muka kammala Azumi 30 na sanar da ku cewa idan Allah ya kawo mu Wannan shekara, shi ma akwai wani Dama na sake samun yin Azumi 30 idan har an ɗauki Azumi a ranar Asabar (02/04/2022).


“Dukkan mu Nigeria da Saudiyya idan Allah ya kaimu ranar 29 ga Watan Ramadan, Wata zai riga Rana Faɗuwa.” a cewar Adamu Ɗan Amurka.


Yanzu dai mahukunta sun bada sanarwar fara duban watan Shawwal a faɗin Najeriya wanda idan har aganshi a ranar Asabar to Lahadi za'a yi sallar idi wanda yai daidai da 1 ga watan Shawwal. Idan kuma ba'a ga watan a ranar Asabar ba to hakan ke nuna ranar Litinin za'a yi sallah.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post