Hotunan Matafiya Jirgin Ƙasan Abuja zuwa Kaduna Da Ƴan Bindiga Suka Yi Garkuwa Dasu


Ƴan bindigar da suka kai hari ga fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa kaduna sun fitar da hotunan wasu daga cikin fasinjoji da suka yi garkuwa dasu wanda yanzu haka suke hannun su.


Maharan dai sun fitar da hotunan fasinjojin a ranar Talata wanda ke nuna matafiyan sun kai kimanin su 41. Yau kusan wata guda kenan da yin garkuwa da matafiyan inda maharan suka kai harin bom tare da buɗe wuta ga fasinjojin wanda yai sanadin mutuwar wasu da dama daga cikin su tare da jikkata wasuA cikin hotunan da ƴan bindigar suka saki ya bayyana yawancin su mata ne su 19 da kuma maza 17 sai kuma ƙananan yara biyar da aka ɗauke su daban-daban. Tuni dai aka tabbatar da mutuwar mutum takwas daga cikin fasinjojin jirgin da ƴan bindiga suka kai wa hari ranar 28 ga watan Maris, 2022.Daga baya ƴan bindigar sun fitar da bidiyon mutanen da ke hannunsu, sannan kuma sun saki mutum ɗaya dag cikin waɗanda sukai garkuwa dashi bayan sun karɓi kuɗin fansa, wanda suke ce tsufansa ne ya sa suka sake shi.


Haryanzu dai ƴan bindigar suna dakon gwamnatin Najeriya da ta sako musu ƴan uwansu da gwamnatin take tsare dasu sannan su saki ragowar al'ummar dake hannun su. Sai dai har kawo yanzu gwamnatin ƙasar ba ta ce komai akan wannan al'amari ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post