Duk Fushin Da Kike Yi Da Mijinki Kada Ki Kuskura Kiyi Masa Waɗannan Abubuwan


Akwai matan da suke wuce gona da iri a lokacin da suka samu matsala da mazansu. Wanda hakan ke jawo ɓacin rai tsakanin ma'auratan. Duk fushin da kika samu kanki a ciki to ki tausasa zuciyar ki. Kada kiyi ƙoƙarin yin wasu abubuwa wanda daga baya kizo kiyi danasani.


Dole ne a riƙa samun matsaloli a tsakanin ma'aurata, amma duk irin matsalar da zaki samu da mijinki kada ki kuskura ki masa waɗannan halayen kamar haka;


(1) Duk irin matsalar da zaku samu da mijinki kada ki shigo da raini a tsakaninku. Ki ci gaba da yi masa biyayya koda kina fushi dashi. Amma shigowa da raini ko ƙasƙantashi saboda kun samu matsala ba naki bane.


(2) Duk irin saɓanin da zaki samu da mijinki kada ki daina yi masa abubuwan da kikasan kina masa waɗanda yake so. Idan duk safiya kece ke zaɓa masa kayan da zai sa, kada ki fasa yimasa masa hakan saboda kina fushi dashi.


(3) Duk ɓacin rai kada ki daina dafawa mijinki abinci. Ko da kece kike taimakon gidan da kuɗin abinci kada ki fasa saboda kun samu matsala.


(4) Akwai matan da idan suna fushi da maigidan sai ya shafi ƴaƴansu. Kada ki cutar da yaranki ko na abokiyar zamanki saboda mijinki ya ɓata miki rai.


(5) Duk tsananin masifan da za ku yi da mijinki idan ya buƙaceki ki miƙa masa kanki ba tare da wani tarzoma ba. Domin kuwa wasu matan idan suna fushi da mazansu sai su ƙi yarda suyi kwanciyar aure dasu. Wannan ba hanya bace da zaki warware matsalarku ba.


Wannan sune kaɗan daga cikin jerin wasu kuskuren da mata suke yi idan sun samu matsala da mazajensu da yakamata su gyara, domin mijinki ne bakida kamar sa kuma shi zaman aure zo mu zauna zo mu saɓa ne. Da fatan mata zasu kiyaye wadannan abubuwan domin samar da ingantancen Zamantakewar aure.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post