Assalam Alaikum warahmatullah wabarakatuh, barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa daku a wannan filin na Duniyarilimi.
A cikin shirin na yau za kuji wasu matsaloli ko kuma wasu kura-kurai da ma'aurata suke aikatawa a rayuwar su ta aure wanda ba su sani ba, da fatan za ku karanta har zuwa ƙarshe.
Aure na iya zama abu mafi ƙololuwar jin daɗi da walwala a rayuwar ɗan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne, wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali hakan duk ya ta'allaƙa ne da waye ko wace abokin auren.
A wannan zamani da mu ke ciki, aure ya zama abinda ya zama a Arewacin Najeriya. Yawaitar mutuwar aure kullum ƙara yawa ya ke. Har ta kai ana iya aure wata ɗaya ko ƙasa da haka a rabu.
Akwai abubuwa masu daɗi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaɓa a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai ƙalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba ɗaya wajen tunkarar sa.
Da yawa a tunanin wasu rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai su iske abun ba haka bane.
Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba ɗayan ta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita cikinta.
Akwai kura-kurai da ma'aurata kan aikata waɗanda ke jawo matsaloli a rayuwar aure, wanda wasu basu ɗauke su a bakin komai ba, daga karshe kuma kan iya jawo mutuwar aure.
Wannan sune jerin kura-kuren da ma'aurata suke yi ba tare da sun sani ba:
(1) Dogon buri;
Da yawan maza da mata kan shiga gidajen auren su da dogon buri, suna tunanin babu komai a cikin rayuwar aure face jin daɗi. Sun ɗauka irin rayuwar fina-finai ce da labaran da suke karantawa a litattafai da abubuwa na jin daɗi da suke gani. Sai dai Kuma kash, wannan rayuwa ce ta zahiri ba tatsuniya ba, rayuwa ce mai tattare da ƙalubale, wata rana zuma wata rana maɗaci.
Dogon burin da ake shiga da shi na daga cikin manyan kura-kurai da ma'aurata ke tafkawa. Sai bayan an shiga a ga akasin abinda ake tsammani, wanda wasu idan an yi sa'a su kan yi hakuri da abinda suka iske, wasu kuwa a lokacin ne fitintinu za su yi ta ɓullowa.
Ya zama wajibi ga ma'aurata su cire dogon buri a rayuwar aurensu, su rungumi abinda suka tarar da hannu biyu da yaƙinin cewa canji na faruwa ne daga kan mutum, sannan idan yayi haƙuri sai yaga canjin.
Kasancewar aboki ko abokiyar rayuwar da wani nakasu a rayuwa ba shi ke nuna cewa rayuwar zamantakewa ta ruguje ba. Kowane ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Haka kowane rayuwar aure bai cika ɗari bisa ɗari ba, dole a samu tawaya ta wani ɓangaren.
(2) Rashin hakuri;
Gaba ɗaya rayuwar aure ɗan hakuri ne, sannan haƙuri shine ribar zaman duniya, duk wanda ba zaiyi haƙuri ba to yana tare da wahala.
Muna cikin wani zamani da ma'aurata kamar jiran juna su ke, kowane a wuya yake danuwansa ya yi abu ya zama abin faɗa da cece-kuce.
Kowane ma'aurata suna samun saɓani a tsakanin junansu, sai dai mi? Wasu kan yi ƙoƙari wajen ganin sun gano bakin zare ta hanyar warware matsalolinsu ta hanyar lumana.
Wasu kuwa a lokacin ne zage-zage, buge-buge da baƙaƙen maganganu ke kunno kai. Daga nan sai wutar ta kara ruruwa, har ta kai ga abinda ba'a so.
Wasu ma'auratan koda su ne da laifi ya kan zama abu mai matuƙar wahala su buɗe baki su bada hakuri. Daga nan sai gardama ta biyo baya. Ko ɗan zaman lafiya bada haƙuri na kashe wutar fitina.
(3) Ɗaukar juna ba a bakin komai ba;
Da yawan ma'aurata ganin an kwana biyu tare, an saba da juna sai ya zama kar ta san kar ne, su kan manta da abubuwan da kan ƙara ma zamantakewar su armashi da nishaɗi.
Zai zamo mace duk abinda mijinta zai yi ba za ta ga bajintar shi ba, tana ganin ai dolen shine yai mata, dan haka ba ta ga abin yabawa ba. Haka ta bangaren maza ma, babu wannan yabawar tsakanin su da matan su.
Yana da kyau komai ƙanƙantar abu da miji ko mata ta/ya yi, a yaba a kuma gode. Hakan zai ƙara ƙarfafa wa mutum. Idan girki tayi, kamata yayi ka gode ma ta, tare da kwarzanta abincin ta, haka bangaren kwalliya ma. Shiyasa wasu matan da sunyi aure, duk wata kwalliya sai su zubar su daina saboda mazajensu ba sa yabawa.
Haka ta bangaren hidimar gida, ya kamata mata su riƙa yabawa mazajensu duk da cewa haƙƙinsu ne su ɗauki nauyin iyalansu, amma yana da kyau a gode mu su. Hakan zai kara mu su ƙarfin gwiwa.
(4) Mantawa da yanda za'a so juna;
Daga zarar anyi aure, duk soyayyar da aka tafka a baya sai ta zama tarihi. Babu sauran soyayya da an yi aure komai ya zama tarihi.
Yana ɗaya daga cikin kura-kuran da ma'aurata ke yi, bayan aure ne ya kamata a ce soyayya ta ƙara ƙarfafa, ba kafin aure ba.
Kowane bangaren mace ko namiji suna da tasu matsalolin. Duk auren da babu soyayya a cikin sa to lallai yana cikin halin rayuwa ko mutuwa.
Rayuwar aure ce ya kamata a ƙawata ta da duk wasu kalaman soyayya, kulawa da kyautatawa, sai dai akasin da ake samu na komi ya zama tarihi. Yana ɗaya daga cikin kura-kurai dake kawo mutuwar aure.
(5) Rashin ba ma juna lokaci;
Daga zarar anyi aure an fara tara iyali kowa ta kanshi yake yi babu wani sauran bawa juna lokaci. Irin wannan ya fi faruwa ga mata, lokacin su kacokam na yaransu ne. Miji da yayi magana za su yi ƙorafin kula da yara da kuma aikace-aikacen gida.
Wasu mazan kuwa aikinsu ya fiye mu su zama da iyalansu har ta kai su na dawowa da aikin office gida.
Daga an gama an gaji sai bacci, babu wani lokaci da ma'auratan suka warewa dan tattaunawa da kuma ƙara kusanci da junansu.
Hakan na saurin kashe aure, sai ka ji mata na maganar "zaman yarana nake, zaman hakuri nake".
(6) Sako wasu cikin al'amuran ku;
Shigowa da wasu mutane cikin matsalolin aure yana ɗaya daga cikin ababen da ke jawo matsala a rayuwar aure. Wasu ma'auratan na da ɗabi'ar kai kukan abokan zaman su ga wasu, wala Allah abokai ne, ƴan uwa ko iyaye a kan abinda bai taka kara ya karya ba.
Irin hakan na rusa aure gaba ɗayan shi, saboda waɗanda ka kai wa ƙarar da irin tunaninsu a kan matsalar da kuke fuskanta.
Shigo da wani cikin rayuwar zamantakewar auren ku na kawo mutuwar aure. Don haka ma'aurata a kiyaye.
Akwai matsalolin da zama daya za ku yi ku warware matsalarku ba tare da wani ya ji ko ya gani ba. Hakan zai taimaka wajen kawo karshen wasu matsalolin.
Ya kamata ma'aurata su koyi warware matsalolinsu a tsakanin su ba tare da sun fitar da shi waje ba. Hakan zai ƙara mu su kusanci a Tsakani saboda sun ɗau juna a matsayin abokai da za su iya zama su tattauna matsalolinsu, sannan su kuma san hanyoyin warware su ba tare da wani ko wata ya shigo cikin lamarin auren ku ba.
(7) Yanke hukunci ba tare da jin ta bakin ɗaya bangaren ba;
Yarda da juna ta sa kuka aminta da junanku a ƙarƙashin inuwa ɗaya, babban kuskure ɗaya bangare ya yanke hukunci ba tare da jin ta bakin ɗayan ba. Shawara na da daɗi musamman ma ga ma'aurata, ya kamata su riƙa shawartar junansu wajen zartar da harkokin rayuwarsu.
Hakan zai sa miji ko mata ganin an girmama su, tunda har za a nemi shawara a wajen su. Hakan na nuna tsantsar yarda da aminta da juna.
Rashin yin hakan ka iya jawo zargi ko wasi-wasi a zuciyar ɗaya, ganin kamar babu yarda a tsakani.
(8) Rashin nuna gaskiya;
Wannan na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar aure a wannan zamanin, duba da shigowar kafofin sada zumunta da za a samu har matan aure nayi.
Ba kowane namiji bane kan aminta matar shi ta shiga Social media ba. Haka mata ma kullum cikin zargin mazajensu suke a dalilin yin hakan.
Babban abinda zamantakewarsu ta rasa shine rashin gaskiya. Idan har kun gina soyayyarku akan gaskiya da wuya irin waɗannan ababen su jawo maku fitina a rayuwar auren ku.
Ko ina namiji ko mace zasu kasance kowane bangare na yi wa ɗan uwanshi kyakkyawar zato. Rashin hakan ya kawo silar mutuwar aurarraki da dama. Duk abinda ma'aurata zasu yi, su yi shi a kan gaskiya da kuma riƙon amana.
(9) Rashin tsayawa juna;
A duk inda ma'aurata suke ya kamata su tsayawa junansu komin wuya komin dadi. Su zama kafaɗar jingina ga junansu wajen share hawayen junansu.
Sai dai mi? Wasu in dai matsala ko damuwa ba tasu ba ce ba, to hakan bai dame su ba, wannan halin ko in kula da su ke nunawa juna na kashe ƙarsashin soyayya, sai ya zama idan shawara ko wata matsala suke ciki maimakon su tuntuɓi juna sai su kai damuwar su wani waje daban.
(10) Kwatantawa kowa muhallinsa;
Wasu kan yi kuskure barin kowa na tsoma baki a rayuwar aurensu. Misali mijin da zai riƙa bari abokan shi na tsara mi shi yanda zai tafiyar da gidanshi, ko mace ƙawayenta su tsara ma ta, koma iyaye su riƙa tsoma baki a rayuwar yaransu.
Miji ko mata dole ne ku nunawa kowanne matsayinsa a rayuwarku da irin muhimmancin da yake da shi, gudun kawo hargitsi a rayuwar aurenku.
Amma matukar aka bar kowa na tsoma baki hakan ba ƙaramin tasiri yake wajen wargaza zaman lafiyar ma'aurata ba.
Daga karshe, za mu iya cewa wadannan sune kaɗan daga cikin manyan kura-kurai da ma’aurata su ke yi wanda ba sa kulawa da su.
Da fatan ma'aurata za'a kiyaye da waɗannan abubuwan da muka lissafi kuma a yi gyara