Rafael Benitez Ya Zama Sabon Kocin Kungiyar Everton


Kungiyar kwallon kafa ta Everton dake buga wasan firimiyar England ta dauki sabon koci Rafael Benitez wanda zai jagoranci kungiyar a kaka mai zuwa.


KARANTA: An bayyana dalilai biyar da suka jawo aka cire Faransa daga gasar Euro

KARANTA: Kasuwar 'yan kwallo, makomar Sergio Ramos da Gareth Bale


Benitez mai shekaru 61 wanda kuma tsohon kocin kungiyar Liverpool ne ya kulla yarjejeniyar kaka uku da Everton.


Sabon kocin na kasar Sifaniya ya maye gurbin Carlo Ancelotti wanda ya ajiye aiki tun a farkon watan Yuni ya koma kungiyar Real Madrid, inda shi ma a can ya maye gurbin Zinedine Zidane.


Kungiyar karshe da Benitez ya horar a Firimiyar Ingila itace Newcastle United, wadda ya ajiye aikin a watan Yunin 2019.


Daga nan ne kuma ya koma horar da kungiyar Dalian Professional FC dake China kuma suka raba gari a watan Janairu bayan shafe watanni 18 tare da Kungiyar.


Everton ta ce Benitez zai soma aikin horar da yan wasan nata yayin da za su dawo wasannin sharar fage a ranar 5 ga watan Yulin 2021.Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post