NBS, Har yanzu tsadar rayuwa na Wahalar da Marasa ƙarfi A Najeriya


Tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da na kayan masarufi na ci gaba da wuju-wuju da marasa ƙarfi a Najeriya, sai dai kuma kisan-mummuƙe ta ke yi, wato a hankula.


KARANTA: An kashe mutum 222 da 'yan bindiga 87 cikin wata uku a Kaduna

KARANTA: Sheikh Abdul-Jabbar Ya Shafe Daren Farko A Gidan Yari


Ƙididdigar farashin kayan abinci da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta yi, ta nuna cewa farashin kayan abinci na ƙara tashi, shi ya sa ko da malejin ƙuncin rayuwa ya ragu, kamar yadda ya ragu zuwa kashi 17.75 a watan Yuni daga kashi 17.93 na watan Mayu, talaka ba zai ji wani canji ba.


Haka dai NBS ta bayyana a cikin rahoton ta da ta fitar a ranar Juma’a.


Ta ce farashin kaya da na ayyukan yau da kullum sun tashi kamar yadda Hukumar Kula da Farashin Kayayyaki (CPI) ya tabbatar a cikin watan Yuni, 2021, zuwa kashi 17.75.


Hakan ya nuna kenan an ɗan samu raguwa da ɗigo 0.18 daga ƙididdigar watan Mayu.


Lissafin dai ya na nufin farashi ya riƙa ƙaruwa a cikin watan Yuni, amma da kaɗan-kaɗan idan aka kwatanta da watan Mayu, 2021.” Inji NBS.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post