Yanzu-yanzu Anyi garkuwa Da Malamai Da Dalibai A Makarantar Nuhu Bamali Dake Zariya


Rahotanni da ke fitowa daga Zariya a jihar Kaduna na nuni da cewa wasu sun afkawa makarantar sannan sukayi garkuwa da mutane a ƙalla mutum takwas a ranar Alhamis da daddare.


KARANTA: 'Ƴan Fashin Daji sun sace mata 60 a Jihar Zamfara

KARANTA: Wani Mutum Daya Bata Sama Da Shekaru 60 Ya Bayyana A Garin Kano

KARANTA: 'Ƴan Fashin Daji sun sace mata 60 a Jihar Zamfara


Rahotannin na nuni da cewa cikin mutanen da aka sace akwai malamai da ɗalibai da kuma iyalan wani malamin makarantar.


Wasu rahotanni na nuni da cewa ɗalibi ɗaya ya rasa ransa sanadiyyar harbin bindiga yayin da wani ya samu rauni.


Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar wa da sashen Hausa na BBc faruwar lamarin kuma ya ce jami'an tsaro sun yi gaggawar zuwa makarantar don tarwatsa maharan.


Sai kuma dai bai bayyana adadin mutanen da akayi garkuwa da su ba.


Makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic ba ta da tazara sosai da sansanin sojoji da ke Jaji a jihar ta Kaduna.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post