Yadda Mutum 13 Suka Rasa Rayukan Su A Hadarin Jirgin Ruwa A Sokoto


Kusan mutane 13 ne suka rasu dukkan su mata ne da kanan yara a cikin wani hadarin jirgin ruwa a Jihar sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya. 


KARANTA: Mun Kashe 'Yan ISWAP Su 50, Inji Sojojin Najeriya

KARANTA: Ku Kashe Duk Wani Wanda Aka Kama Da Bindiga, Gwamna Matawalle

KARANTA: Hadin Sa Kishiya Tagumi


Shafin Bbc Hausa dai ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis a yankin karamar hukumar Shagari da ke kudancin jihar ta Sakkwato.

Hadarin dai ya faru ne mako daya daidai bayan da wani hadarin jirgin ruwa ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100 a makwabciyar jihar Kebbi.

Kamar lamarin da ya faru makon jiya daura da garin Warah na jihar Kabbi, kwale-kwalen ya kife ne lokacin da matafiyan ke da kusa da kai wa inda za su domin bikin aure.

Jirgin dai ya taso ne daga garin Ginga dauke da mutum 18, amma sai ya kife daf da ƙauye Doruwa inda ya nufa; lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 13 yayin da biyar suka tsira.

Alhaji Aliyu Dantine Shagari shi ne shugaban karamar hukumar Shagari inda lamarin ya faru kuma ya ce tuni dai suka yi jana'izar wadanda suka rasu.

Yayin wata ta'aziyya da ya kai a garin Ginga inda mamatan suka fito a dazu, gwamnan jihar ta Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya  samar wa al'umomin yankin da jiragen ruwa na zamani masu amfani da inji da kuma rigunan hana nutsewa a ruwa don kare afkuwar hakan a gaba.

Ko a watan Agustan bara ma kusan mutane tara ne suka rasa rayukansu a cikin hadarin jirgin ruwa makamancin wannan a yankin karamar hukumar Goronyo da ke gabashin jihar ta Sakkwato.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post