Cutar Korona Tana Cigaba Da Kashe Mutane A Najeriya


Cutar korona ta sake kashe mutum 18 a Najeriya Kamar yadda hukumar NCDC ta bayyana. 


KARANTA: Mun Kashe 'Yan ISWAP Su 50, Inji Sojojin Najeriya

KARANTA: Ku Kashe Duk Wani Wanda Aka Kama Da Bindiga, Gwamna Matawalle

KARANTA: Mayakan ISWAP Sun Mamaye Al'ummar Borno, Sun Afkawa Sojojin Najeriya


Ƙarin mutum 18 sun ras ransu a ranar Alhamis a Najeriya sakamakon cutar korona, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.


Zuwa yanzu sabbin alƙaluma sun sa adadin waɗanda suka rasu daga cutar zuwa 2,117. Kamar yadda shafin Bbc Hausa suka wallafa. 


Kazalika, wasu mutum 122 sun kamu da cutar a jihohi tara. Wanda Jihohin sun haɗa da Leags (105) da Imo (4) da Kaduna (4) da Akwa Ibom (3) da Abuja (2) da Delta (1) da Rivers (1) da Oyo (1) da Ekiti (1).


Zuwa yanzu, jumillar mutum 166,682 ne suka kamu da cutar sannan aka sallami 162,521 bayan sun warke.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post