Wani Mutum mai shekaru casa'in da uku da ake zaton ya mutu ya dawo gida Kano bayan shekaru 67.
KARANTA: Dalilai biyar da suka tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau
KARANTA: Yadda Mutum 13 Suka Rasa Rayukan Su A Hadarin Jirgin Ruwa A Sokoto
KARANTA: Mun Kashe 'Yan ISWAP Su 50, Inji Sojojin Najeriya
Mutumin da ake zaton ya mutu kafin samun 'yancin kan Najeriya a shekarar 1960 ya koma gida a jihar Kano bayan shafe shekaru 67 a garin Ibadan.
An ce Sa'idu Abdullahi mai shekaru casa'in da uku ya bar kauyen su na, Dakatsalle, a cikin Karamar Hukumar Bebeji dake a jihar Kano shekarar 1953, a zamanin marigayi Sarki Abdullahi Bayero.
An ce ya koma Ibadan, a Kudu maso Yammacin Nijeriya inda ya zauna tsawon shekaru 67, har sai da ya dawo gida Dakatsalle, a makon da ya gabata.
Gidan su Sa'idu ya juya tamkar zuwa makka don mutanen gari, wadanda ke zuwa wurin don ganin mutumin da ake tunanin ya mutu sama da shekaru 60 da suka gabata.
Sa'idu, wanda ya bar gida lokacin yana da shekaru 26 ya dawo gida a Arewa maso yamma yana da shekaru 93 bayan ya kwashe shekaru 67 a Ibadan.
A hirar su da yake zantawa da jaridar Sahara Reporters a cikin harshen Hausa, Sa'idu ya ce, "Na dade, ina son komawa gida; wanda na baro kafin samun 'yancin kan Najeriya.
"Na bar Dakatsalle tun ina da shekaru 26, a matsayin saurayi mai kuzari, a zamanin Sarki Abdullahi Bayero na Kano, wanda mulkinsa ya fara a 1926 zuwa 1953.
"Na sake komawa garin Ibadan domin cinikin goro sannan kuma na samu kawuna na wajen mahaifiyata wanda ya bar gida da wuri a irin wannan yanayi.
"Tunda na baro gida na zauna a garin Ibadan, ban kuma sa kafata a gidan mu ba sai a wannan karon cikin shekaru 60 da suka gabata."
Akwai hawayen farin ciki da murna yayin da yara da jikokin 'yan uwansa, da maƙwabta suke nuna murnar dawowar mutumin da suke tsammanin ya mutu.