Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Rayuwar Marigayi Sani Abacha

 


Ga Wasu Daga Cikin Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Rayuwar Marigayi General Sani Abacha 


KARANTA:  'Ƴan Fashin Daji sun sace mata 60 a Jihar Zamfara

KARANTA: Wani Mutum Daya Bata Sama Da Shekaru 60 Ya Bayyana A Garin Kano

KARANTA: Dalilai biyar da suka tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau


Shekara 20 kenan da mutuwar shugaban mulkin soja na Najeriya Gen Sani Abacha

An zargi gwamnatinsa da yin kama-karya da kuma take hakkin dan adam.

Har yanzu ra'ayoyin mutane da dama sun bambanta a kan Sani Abacha a Najeriya. Shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda shi ma ya taba yin mulkin soja, ya yabe shi da cewa ya samar da ci gaba kamar gina tituna da bunkasa harkar ilimi da lafiya.

Ga dai wasu daga cikin muhimman abubuwa dangane da rayuwar marigayin:




An haifi Gen Sani Abacha a jihar Kano dake arewacin Najeriya a shekarar 1943.

Ya kammala makarantar horon aikin soji dake Kaduna a shekarar 1963, ya kuma samu Karine horo a kasar Burtaniya.


A shekarar 1965 ya auri Maryam Jiddah. Sunana da 'ya'ya 10 tare, amma babban cikin su ya mutu.


A shekarar 1985 An hambarar da gwamnatin Janar Buhari da sa hannun Abacha. Ya kuma taimaka an dora Janar Ibrahim Babangida a mulkin kasar, shi kuma aka kara masa girma zuwa Manjo Janar.


A ranar 12 ga watan Yuni 1993 a n gudanar da zabe don mika mulki ga farar hula kamar yadda aka dade ana jira. Kuma sakamakon farko-farko ya nuna cewa mashahurin mai kudin nan Moshood Abiola ke kan gaba, Janar Babangida ya soke sakamakon zaben.


A watan August na 1993 An nada Abacha Ministan Tsaro, bayan da Babangida ya sauka ya kuma samar da gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Ernest Shonekan.


A ranar 17 ga watan Nuwamba 1993 Shonekan ya yi murabus ya kuma mika mulki ga Abacha, a wani al'amari da mafi yawan mutane ke ganin kamar wani juyin mulkin ne. Ana ganin mulkinsa na cike da cin zarafin bil'adam da take 'yancin fadin albarkacin baki.


A shekarar 1994 Moshood Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa saboda cin zaben da 'ya 'yi' amma an kulle shi.


A shekarar 1995 Mulkin Abacha ya fuskanci Allah-wadai daga kasashen duniya da dama kuma an dakatar da Najeriya daga kungiyar kasashe renon Ingila bayan da aka kashe masu kula da muhalli tara daga yankin Ogoni, wadanda suke zanga-zangar adawa da ayyukan gwamnati da kamfanin mai na Shell. Daga cikinsu akwai Ken Saro-Wiwa, wani mai rubuta wake, wanda kuma aka zaba cikin wadanda za a bai wa lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.



A shekarar 1996 Africa ta yamma  An zabi Abacha shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin kasashen Yankin Afirka Ta Yamma (Ecowas).


A watan Fabrairu 1998 Abacha ya tura dakarun Najeriya zuwa Saliyo a wani kokari na hambarar da gwamnatin mulkin soja da kuma dawo da gwamnatin farar hula wacce aka hambarar shekara guda kafin nan.


8 ga watan Yuni shekarar 1998 Abacha ya mutu sakamakon bugun zuciya da ake zargin shi ya yi sanadinsa, an kuma binne shi a wannan ranar. Shekara guda bayan nan ne Najeriya ta koma kan turbar dimukradiya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post