Illolin kallon fina-finan batsa


Kallon tsaraici haramun ne a shari'ar musulunci in banda na matarka ko na mijinki ballantana kuma kallon saduwa tsakanin Mazinata wannan abune mai matukar muni sosai. 


KARANTA: Mahaifiyata ta Rasu Ana binta Azumi, Shin Zamu iya rama mata?

KARANTA: Ni mace ce mai matsananciyar sha'awa maziyyi yana yawan fitomin ta gabana

KARANTA: Bambancin maniyyin namiji da maniyyin mace


Allah yana cewa: "Ka gayawa muminai maza su rintse idanuwansu daga kallon haram kuma su kiyaye farjinsu daga yin zina. Yan uwa mu kiyaye, duk wanda yake kallon irin wandannan abubuwa to lalle yayiwa Allah tawaye.


 A wani gurin Allah yana cewa:- Kada ku kusanci zina hakika ita zina Alfasha ne kuma mummunan hanyace. 


Kunga saboda halakar da take cikin zina sai Allah yace kada mu kusan ceta, shi kuwa irin wannan kallon yakan sanya masu yinsa su afka cikin zina kai tsaye. Manzon Allah (S. A. W) yana cewa: "Allah ya tsinewa mai kallon tsaraici da kuma wanda ake kallon tsaraicin nasa.


 Daga karshe ina kara jawo hankalin masu yi su tuba su daina.......!!! Dan Allah Daure ka tura wannan sakon zuwa ga sauran yan uwa domin baka san wanda zai shiryu ba ta sanadin ka.


 Ya Allah ka tsarkake mana zukatanmu, ka Kare zuri'ar mu daga Afkawa cikin mummunar bala'i amen. 

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post