An Kashe 'Yan Bindiga Su 80 Bayan Sace Dalibai Da dama A Jihar Kebbi

 


An Kashe 'Yan Bindiga Su 80 Bayan Sace Dalibai Da dama A Jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya 


KARANTA: Wani Mutum Ya Mutu Yayin Da Yake Jima'i Da Matar Abokinsa

KARANTA: Yadda Ƴan bindiga suka kashe ƴan sanda huɗu a jihar Zamfara

KARANTA: Jiragen Yaki Na Sojoji Sun Kashe Sama da Shanu 1,000 A Nasarawa


Rohotanni daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na nuna cewa wasu jami'an tsaro a ƙasar sun kashe 'yan fashi kusan su 80 a kokarin su na kuɓutar da yara 'yan makaranta da 'yan bindiga suka sace.


Sashin Jaridar Hausa na Bbc ya rawaito cewa a ranar Alhamis da rana ne 'yan bindigar suka kai farmaki a makarantar FGC Yauri tare da sace daliban.


Sai dai, sojoji sun kuɓutar da wasu daga cikin yaran.


Wasu shaidu sun shaida cewa sun ga gawar ɓarayin dajin fiye da guda 80 a kwance a kasa.


Suka ƙara da cewa an yi bata kashi sosai a tsakanin dakarun tsaro da ɓarayin dajin a Ƙaramar Hukumar Sakaba ta jihar Kebbin.


Wanda abin ya faru akan Idon su sun ce 'yan bindigar sun tafi da dalibai da yawa sannan suka harbi wasu daga cikinsu.


Wani mutum da ya ga lokacin da lamarin ya faru ya fadawa sashen hausa na bbc hausa cewa 'yan bindigar sun ci karfin 'yan sandan da ke gadin makarantar kana suka kwace motoci kirar Toyota Hilux daga wurinsu suka zuba daliban sannan suka tafi da su.


Wasu mutane sun ce an kai dalibai da dama asibiti domin yi musu maganin harbin bindiga sakamakon raunukan da suka ji a yayin da suke tserewa daga harin na 'yan bindiga.


Wani dan majalisa da ke wakiltar yankin a Majalisar Wakilan Najeriya, Muhammad Bello Ingaski, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun sace dalibai maza da mata.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post