Gwamnatin Zamfara Ta Dakatar Da Sarkin Zurmi Kan Zargin Alaka Da 'Yan Ta'adda


Gwamnatin Zamfara Ta Dakatar Da Sarkin Zurmi Kan Zargin Alaka Da 'Yan Ta'adda 


KARANTA: Buhari Yayi Magana Kan Shirye-shiryensa Bayan Ya Sauka Daga Mulki A 2023

KARANTA: Wannan Hadin Na Amare Ne Zalla Da 'Yan Matan Da Zasuyi Aure

KARANTA: Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Rayuwar Marigayi Sani Abacha


Gwamnan jihar Zamfara dake arewa maso yamma ya dakatar da Sarkin Zurmi, Atiku Muhammad, bisa zargin sa da hannu a kashe-Kashen da 'yan fashin daji suke yi a yankin masarautar tasa.


A wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar tace gwamna Bello Matawalle ya kafa Kwamitin bincike a kan zarge-zargen da ake yiwa basaraken.


Haka zalika, an umarci Bunun kanwa, Bello Sulaiman, akan ya karbi jagorancin masarautar anan take.


Wannan na zuwa ne kasa da mako biyu bayan gwamnatin Zamfara ta dakatar Dan Sadau, Alhaji Hussaini Umar, bisa zargin alaka da 'yan bindigar dake addabar yankin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post