Nayi jima'i a Ramadan, amma bazan iya kaffara ba, Ko zata fadi a kaina?


NA YI JIMA'I A  RAMADHANA, AMMA BA ZAN IYA KAFFARA BA, KO ZA TA FADI A KAINA ? 


KARANTA: Shin zamu iya yin jima’i da daddare muyi wanka kafin muyi sahur?

KARANTA: Banaso nasha azumi Ko zan iya shan maganin hana haila?

KARANTA: Banyi bude baki ba na Sadu da Matata, ya matsayin Azumi na yake?


Tambaya

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuh! 

Malam Ina da tambaya game da Hadisin manzon Allah (SAW)akan wani mutum da ya sadu da matar sa da rana cikin Ramadan, duba game da yadda Manzon Allah ya warware masa matsalar sa, to idan har an sami wani ya sadu da matar sa  da Azumin kuma bazai iya azumiba,'yanta wuyaye, ciyarwar ba kuma bai sami wanda zai ba shi abin da zai ciyar ba, yaya zaiyi. Allah ya saka da alkairi.


Amsa


Wa'alaikum assalam warahmatullah wabarakatuh! 

To dan'uwa kissar da ka fada ta zo a hadisi tabbatacce mai lamba ta: 616 a cikin  Sahihil Bukhari, saidai malamai sun yi sabani akan mas'alar zuwa zantuttuka guda biyu : 


1. Kaffarar ba za ta fadi akansa ba, za ta wanzu har zuwa lokacin da zai samu damar yin daya daga cikinsu, kamar yadda suke a jere a hadisin, saboda annabi s.aw. a cikin hadisin bai ce masa kaffara ta fadi akansa ba, ya yi masa shiru ne.


2. Kaffarar ta fadi akansa, saboda lokacin ya ce ba zai iyaba, Annabi s.a.w ya bar masa dabinon don ya ciyar da iyalansa.

Wasu malaman suna rinjayar da zance na karshe, saboda shi ne ya fi dacewa da zahirin hadisin .

Allah ne mafi sani Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post