Mace mai haila zata iya yin kowace ibadah a watan Ramadan


MACE MAI HAILA A WATAN RAMADANA?


KARANTA:Nayi jima'i a Ramadan, amma bazan iya kaffara ba, Ko zata fadi a kaina?

KARANTA:Mahaifiyata ta Rasu Ana binta Azumi, Shin Zamu iya rama mata?

KARANTA: An gargadi mata da su daina aske gashin gaban su, domin hakan yana jawo matsala ta kiwon lafiya


"Mace mai haila zata iya yin kowace nau'in ibadah in banda sallah, azumi, kewaya ka'abah, da kuma yin i'itikafi a masallaci"


"Babu wani laifi gameda mace mai haila tayi wa kanta ruq'yah ta hanyar karanta alƙur'ani, ko sauraron addu'oi, da zikirori waɗanda wajibai ne a musulunci, sannan kuma babu laifi ta karanta mus'hafi a matsayin da ba sai ta kai ga taɓa mus'hafin ba face sai da shamaki"

IslamQA.info. Fatawa no 152742


"Mace mai haila zata iya yin istigfãri, (neman gafarar Allah) ta hanyar maimaita faɗin A'stagfirullah!, (ina neman gafarar Allah), da kuma sauran addu'oin da suka tabbata acikin alƙur'ani da sunnah"


"Zata iya yin addu'a, ta roƙi Allah dukkanin abu mai kyau da take buƙata anan duniya da kuma lahira, domin itama addu'a ai ibadah ce"


"Manzon Allah ﷺ, yace: addu'a itama ibadah ce"

Sunan Abi Dawud (1479)


"Zata iya yin zikirori kamar faɗin: SubhanAllah, Wal-Hamdulillah, Wala-Ilaha-ilLallah, Alhamdulillah, da makamancin hakan, waɗanda suka tabbata a Qur'ani da sunnah"



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post