An Kashe Makiyayi Daya da Shanu 52 A Sabon Harin Filato


An kashe wani makiyayi daya kuma an bayyana batan wani a Kauyen Maiyanga da ke gundumar Kwal a karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.


KARANTA: Wasu hanyoyi 8 da zaka kiyaye lafiyar maniyyinka

KARANTA: Mata shin sau nawa kuke duba lafiyar farjinku a rana, ga wasu hanyoyi da zasu taimaka muku

KARANTA: Abinda Buhari ya kamata yayi a harkar tsaro, Ibrahim Babangida


Shugaban kungiyar Miyyetti Allah (MACBAN), Malam Nura Abdullahi, ya ce an kashe mamacin a ranar Alhamis kuma aka jefa shi a cikin wata rijiya da ke kusa da yankin.

Shugaban ya bayyana cewa “Umar Muhammad Musa mai shekaru 40 ya shiga hannu ne yayin da wasu maharan suka kashe shi a lokacin da yake kan hanyarsa ta kai wa yaransa abinci wadanda ke kiwon shanun sa a wani kauye da ke kusa da Kuru a karamar hukumar Jos ta Kudu.”


Ya ce an sace shanu 52 sannan daga baya aka gano gawarwakinsu a kauyen Maiyanga na karamar hukumar Bassa da ke jihar, ya kara da cewa makiyayin da ya bata shi ne yake kiwon shanun.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wakilin Jami’in ’Yan sanda na Gundumar, Barkin Ladi, da kuma kwamanda na 6 na rundunar tsaro ta Haven, Col. AH Gwani, sun halarci jana’izar.


A cewar Abdullahi, an kashe Umar ne a ranar Alhamis din da ta gabata, amma an gano gawarsa tare da mai taimaka wa ’yan sanda da kuma Ofishin Tsaro na Tsaro.

Ya kara da cewa "An gano gawarsa daure da duwatsu, an jefa ta cikin rijiya, an yi amfani da injina guda uku wajen fitar da ruwa kafin a kwashe gawar,"


Malam Nura ya ce an fara sace shanun 52 ne a ranar Lahadi a kauyen Maiyanga da ke gundumar Kwall a karamar Hukumar Bassa.


"An gano gawarwakinsu sun mutu a wani daji da ke kusa," in ji shi.

Shugaban kungiyar ta Miyyetti Allah (MACBAN) na yankin Barkin Ladi, Alhaji Shuaibu Bayaro, ya roki jami’an tsaro da Gwamnati da su dauki matakan da suka dace, yana mai cewa “Ina kira ga matasanmu da su yi hakuri kada su dauki doka a hannunsu. Ya kamata mu bar tsaro da Gwamnati suyi aikinsu, amma a lokaci guda muna neman a yi adalci. ”


Lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, ASP Ubah Gabriel, ya ce zai yi bincike tare da komawa ga wakilinmu amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi hakan ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post