YAU AKE CIKA SHEKARA DAYA DA RASUWAR MALAM ABBA KYARI

YAU AKE CIKA SHEKARA DAYA DA RASUWAR TSOHON SHUGABAN MA'AIKATA NA FADAR GWAMNATIN TARAYYA, MALAM ABBA KYARI

Tsohon shugaban fadar gwamnatin Nigeria Malam Abba kyari a yaune yake cika sheakar daya cif da rasuwa.

Shi dai Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilu na shekara 2020 sakamakon rashin lafiya wacce ake kyauta zaton cewa cutar corona ce tai sanadin rasuwar sa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayin a matsayin babban aminin sa na jiki mai kishin kasa.

Shugaba Buhari ya Kara da cewa Abba kyari aminin sa ne tun tsawon shekaru 42 da suka gabata suna tare kafin daga bisani ya zama shugaban ma'aikata a fadar sa.

Shi dai malam Abba kyari ya rasu ne yana da kimanin shekaru 67 a duniya.

Muna Adduar Allah ya jikansa da sauran wanda suka gabata amen. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post