MINISTAN WUTAR LANTARKI YA NEMI AFUWAR YAN NIGERIA DALILIN RASHIN WUTA



DALILIN RASHIN WUTAR LANTARKI A NIGERIA 


Ministan lantarki Injiya Sale Mamman ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan rashin samun wuta yana mai cewa nan ba da jimawa ba komai zai gyaru ya koma dai_dai a cewar sa.

Ministan dai ya alaƙanta rashin wutar da ake fama da shi, da matsalolin da ake fuskanta a cibiyoyin raba wutar lantarki guda takwas na ƙasar.

Sannan kuma ya ce an rufe cibiyar wuta ta Jebba domin yin wasu gyare-gyare da a kan yi kowacce shekara.

Haka zalika ya bayyana wasu ciboyoyi bakwai da suka hada da Geregu, Sapele, Omotosho,  Gbarain, Omuku, Paras da Alaoji da ya ce suna fama da ƙarancin iskar gas, yayin da da tashar samar da wuta daga ruwa ta Shiroro ke buƙatar gyara inji ministan. 

Related
Previous article
Next article

Ads Atas Artikel

Ads Tengah Artikel 1

Ads Tengah Artikel 2

Ads Bawah Artikel