AMFANIN SHAN KUNUN AYA GA JIKIN MU

KO KUN SAN AMFANIN SHAN KUNUN AYA GA LAFIYAR JIKIN MU? 

Aya wacce muka sani a kasar Hausa ana kiranta da suna tigernut a harshen Turanci, Yarubawa na kiranta da suna Ofio, a yayinda su kuma Kabilar Igbo suke kiranta da suna imumu ko aki.

An Samun aya a sassa daban-daban a kasashen duniya ciki harda Nigeria.

A can baya, an dauki aya tamkar kayan kwalamane kawai wanda yara ke ci dan jin zaqi ga bakinsu wanda yasa har daquwar ayar ake yi ana siyarwa. Wannan baya rasa nasaba da rashin samun cikakken bayanin almfanin Aya. Daga bisani sai kimiyya ta bankado binciken wasu masana akan dimbin amfanin aya wanda jin haka yasa har kunun aya ake yi a yanzu.

Sai dai kuma har zuwa yanzu akwai mutane da dama da basu san amfanin shan kunun aya ba, inda wasu sun dauka abinsha ne kawai maganin yunwa ko kayan marmari. Wasu ma kayan zaqi suka dauke shi.


Ganin haka yasa na zo maku da bayani dalla-dalla a kan aya da kuma amfaninta.


Aya tana kunshe da wasu muhimman sinadirai na musamman dake gina jiki, masu inganta lafiyar jinin jiki da tsokar gangar jikin dan adam masu kare jiki daga kamuwa da wasu kwayoyin cuta, masu maganin wasu illoli da matsalolin dake damun maza da mata da makamatansu.

Kadan daga cikin wadannan sinadiran sun hada da: Phosphorus,vitamin, Fat, protein, dietry Fibre, potassium, zinc, sodium, calcium, magnesium, copper, vitaminC, da carbohydrates.

Anyi amanna cewa aya tana sanya jini kaiwa da kawowa a cikin kowane lungu da sako na jiyojin jiki (proper circulation) wanda a dalilin haka yasa ake ganin tana karin sha'awa da karfin zakari ga namiji domin jiyojin zakari zasu rinka samun jini wadatacce da zai rinka kaiwa da kawowa.


Aya tana samarwa jiki da wadataccen sinadirin Vitamin E da vitamin C da kuma Zinc da sinadirin quercetin wanda suke da matukar amfani ga mace ko namiji musamman masu neman haihuwa.

Aya tana kara yawan ruwan maniyi da kuma lafiyarsa (quantity and quality sperm count) ga namijin da ruwan maniyinsa suka ja baya ko yake fama da karamcin 'ya'yan maniyi a jiki(low sperm count)

Aya karawa mata ni'ima-


Ga yadda ake yin wannan hadin na kunun Aya Kamar haka

A nemi ayar misalin gongonin madara daya da kuma garin dabino rabin gongoni sai a hada da ciyarwa nan da ake kira dan hakin daka raina sai a dake a maidata daquwa ko a maidasu tamkar alawa a ringa ci, kada a saka suga ko kadan.

Aya tana kara yawan ruwan maniyi ga namiji sai a nemi garin aya gongoni daya sai a sanya ruwan kwakwa a dame garin a ringa sha.

Aya na samarda yawan oestrogen wanda karancinsa na haifar da rashin haihuwa ga mata.

Aya na samarda testosterone wanda shi ne male sex hormone, inda yai karancin ga jikin namiji to zai kasance baya da sha'awa tamkar bai balaga ba, zai ga yana ramewa kuma zakarinsa baya karuwa haka kuma zai kasance baya da maniyi lafiyayye wanda wannan zai hana shi haihuwa.

Aya tana samarda sinadiran vitamin E ga jiki wadanda ke kara yawaitar maniyi da kuma lafiyar sa.

Wadnda ke taimakawa mata samun damar dasa qwai (ovulation) wanda rashin yin ovulating ko rashin dasa qwai ga mace zai hanata daukan juna biyu. Wannan dalilin ne yasa  matan da suka tsufa basa daukan juna biyu domin sun daina dasa kwai.

Mata da kuma mazan da suke da qalubale na rashin samun haihuwa sai su rinka amfani da aya akai-akai.

Amma fa a kaucewa amfani da SUGA, wannna natural drink ne akoi suga ta daban a ciki da bata bukatar wata suga can ta daban.

Aya na kara yawan ruwan nono, dan haka ga duk macen dake shayarwa sai ta rinka amfani da kunun aya akai-akai bayan taci abinci.

Mazan dake neman amfanuwa da aya sai a ringa hada garinta dana citta a nike sai sun koma gari sai a sanya babban cokali biyu a cikin zuma a sha.

Idan anci abinci to sai a nemi cup daya na kunun aya a sha hakan zai taimakawa ciki dan saurin narkarda abinci.

Idan aka hada garin tafarnuwa dana citta da garin aya aka dama a tare da zuma zai bada wasu magungunnan na daban wadanda za muyi bayaninsu nan zuwa gaba. 

Mai fama da bayan gari mai tauri kamarna dabbobi to sai ya rage cin shinkafa da abinci mai karfi sai ya  shan diyan itatuwa daga bisani yabiyo baya da shan kunun aya.

Kada a hada kunun aya da madara wanda hakan zai sa concentration din yayi yawa yana ma iya zama wani abu na daban da baidace da lafiya ba.

Kada a sanya suga. 

Kada a tafasa 

za a iya hada kwakwa ko dabino a madadin suga.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post