ANYI GARKUWA DA WASU MA'AIKATAN LAFIYA A JIHAR KADUNA




Lamarin ya faru ne Jim kadan bayan da wasu 'yan bindiga sun kai hari a jami'ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, wanda rahotanni suka nuna an sace dalibai da dama a makarantar.

Daga jaridar VOA Hausa, sun rawaito cewa masu garkuwa da mutane, sun kai hari a wani asbiti dake karamar hukumar Kajuru dake garin Kaduna a arewacin Nigeria, inda sukayi awon gaba da wasu ma'aikatan jinya su biyu.

Abin ya faru ne a babban asibitin Idon wanda ke da tazarar tafiyar kasa da kilomita daya da wani shigen binkicen 'yan sanda akan hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Lamarin ya faru ne sa'oi kadan bayan da wasu' 'yan bindiga suka kai hari a jami'ar Greenfield dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda rahotanni suka nuna an sace dalibai da dama.

Shugaban karamar hukumar Kajuru Cafra Casino, wanda ya tabbatar da aukuwar hakan, inda ya nemi da jama'a su kwantar da hankalin su.

Rahotanni sun nuna cewa da sanyin safiyar ranar Alhamis ne maharan suka kai wannan harin yayin da wasu ke cewa a daren Laraba aka kai harin.

Matsalar rashin tsaro da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin arewa maso yammacin Nigeria, lamarin da yasa akaita rufe makarantu, mutane suka kauracewa gonaki da manyan hanyoyi dake yankin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post