SIFFOFI SHA ƊAYA DA MACE TA KE SO DAGA WAJEN NAMIJI


SIFFOFI SHA ƊAYA DA MACE TA KE SO DAGA NAMIJI 

Wata mace mai suna Amira Hassan Addasuqy ta yi wani bincike ranar 27/2/2017 a wani shafi mai suna الحب والعلاقات ة'. An yi binciken ne kan wasu suffofi guda sha ɗaya da mace take so namiji ya  zamo yana da su.

 

1. Namiji mai tausayi. Mace tana son namiji mai tausayi ba mai kaushin zuciya ba da saurin duka. Tana son mutum ya zamo ko faɗa zai mata ya yi cikin hikima.

 

2. Mace tana son wanda zai girmama ta ba wanda zai tozarta ta da gori ba. 

 

3. Mace tana son namiji ƙaƙƙarfa mai lafiyar da zai biya mata buƙata ta aure.

 

4. Mace tana son namijin da yake amsa kuskurensa idan ya aikata.

 

5. Tana son namiji mai karamci, alheri ba ƙanƙamo ba.

 

6. Mace tana son namijin da ya yarda da kansa.

 

7. Ba ta son namiji mai nauyin jiki da kasa wanda zai ta wahalar da ita.

 

8. Mace tana son namijin da zai sa ta farin ciki ta ji cewar ta cika mace. Ba wanda in ya doso gida za ta dinga fargaba ba, ba za ta sake walwala ba sai ya fita.

 

9. Tana son namijin da ke son ta don Allah ba don dukiya, matsayi ko kyanta ba. Domin ta san idan waɗannan abubuwa suka ƙare watsar da ita zai yi.

 

10. Mace tana son namiji mai wayo kuma mai haƙuri.

 

11. Tana son namiji mai dogon tunani kafin ya yanke hukunci. Wanda ko rai ta ɓata masa ba zai yanke hukunci ba sai ya yi tunani.

Wannan wani bincike ne da mace ta gabatar, da fatan maza za su ɗauki darasi.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post