IRIN MATAR DA YA KAMATA KA AURA


IRIN MATAR DA YA KAMATA A AURA.


Kafin mutum ya yanke shawarar yin aure ya kamata ya bi matakai guda uku. 

Na farko ya yi istikharah wato neman zaɓi daga wajan Allah, yayi salla raka'a biyu, kamar yadda yazo a hadisin Jabir ɗan Abdullahi daga riwayar Bukhari 1166, bayan yayi sallama (wasu malamai suna ganin za a iya yin wannan addu'a kafin sallama, kamar shekhul Islam Ibn Taimiyya ) sai ya ƙaranta wannan addu'a ta neman zaɓi daga Allah.

Na biyu. Ya nemi shawara daga masana addini da ɗabi'u da halayya, da gogayya da harkokin aure, domin su bashi shawara bayan sun saurare shi sunji irin tasa buƙatar, wanda yake shawara ba zai yi nadama ba. 

Na uku. Dole mai neman aure mace ko namiji su cire son zuciya idan su na neman aure na gari, duk da shari'a ba ta yarda mutum ya auri matar da baya so ba, amma mafi yawan mata na gari basu fiye kyau da yawa ba, don haka idan an sami mace mai kyau amma ba ta da tarbiyya, da mai addini da tarbiyya amma tana da ƙarancin kyau sai ka ga an raba hankalin mai neman aure.

Manzon Allah saw yace :Ana auran mace saboda abu huɗu, saboda kyawunta ko kudinta ko matsayin ta ko addininta, ka rabauta da mai addini, idan ka ƙi hannun ka yayi turɓaya. Bukhari 5090. Daga Abu Hurairah RA. 

Waɗannan  abubuwa guda huɗu sune mafi yawan masu neman aure suka fi buƙata ga mace, amma ana samun wata ta haɗa dukkan waɗannan siffofin, wata kuma ta sami uku daga ciki, wata ta sami biyu wata siffa ɗaya kawai take da ita daga cikin waɗannan siffofin. 

Wacce tafi itace wacce ta haɗa dukkan waɗannan siffofin 

1, mai kyau mai kuɗi mai matsayi mai addini dukkan huɗun tana da shi. 

2, Mai addini da kyau. 

3, Mai matsayi da kuɗi amma babu kyau babu addini. 

4, Mai addini amma babu kudi.

5. Kyakkyawa amma babu tarbiyya ta addini.

6. Mace tana da siffofi guda biyu na fili kamar kyau da muni ko baƙi da fari ko tsawo da gajarta, a kwai kuma siffofi na ɓoye kamar kirki da hakuri da tarbiyya da juriya da iya zaman aure.

Mafi yawan mutane sunfi son mace mai kyau, wannan kuwa ba laifi bane, amma idan mutum ya auri mace saboda kyawun ta kawai, lokacin da kyawun ya tafi, sai Kaga mace tana samun canji daga mijinta, saboda abinda ake son ta saboda shi ya tafi ko ya ƙare, kuma mace mai kyau kawai babu tarbiyya sunfi wahalar da mazan su da halakar da su, domin za su dinga yin abinda be kamata ba. a wasu lokuta domin su faranta musu ko da hakan ya saɓawa Allah da Manzon sa. 

Kowa cikin masu neman aure daga cikin maza ko mata akwai siffofin na fili da yake sha'awa daga matar da yake so ya aura, ko daga mijin da take so ta aura, kamar fara ko baƙa ko doguwa ko gajeriya, mai ƙiba ko siririya,  kyakkyawa ko Mummuna, amma shi kyau da muni ya dangana ne da abinda mutum yake so, domin mummuna a wajan wani kyakkyawa ne, kuma kyakkyawa a wajan wani mummuna ne.

Ya tabbata a hadisi daga Maa'ƙalu ɗan yasar yace : wani mutum yazo wajan Manzon Allah saw, sai yace :Na sami wata mata zan aura tana da matsayi kuma mai kyau ce, na iya auran ta? sai yace masa a'a, bayan lokaci sai ya dawo ya kuma yin wannan tambaya ya ƙara ce masa a'a, a karo na uku sai yace masa : Ku auri mai iya soyayya mai haihuwa, domin zan yawaici al'umma da ku. Abu Dauda 2050. Nasaiy 3227. Silsila Na Albaniy. 2373.


Wannan hadisi ya zo da ƙarin siffofi guda biyu sune soyayya da haihuwa, yaya za a yi zaman soyayya, kuma a haifi ƴaƴa ayi musu kyakkyawan reno, don haka muna iya ƙara waɗannan siffofi akan na farko su zama siffofi shida

Akwai wani hadisi ya zo daga Abdullahi ɗan Amri, yace :Manzon Allah saw yace : Duniya wani jin daɗi ce, mafi jin daɗin duniya shine samun mace ta gari, Muslim ya ruwaito. sai aka fassara mace ta gari a wata riwayar da Tirmiziy ya ruwaito da  siffofi guda biyar, wacce idan ka kalle ta za ta faranta maka rai, idan ka bata umarni za ta yi maka biyayya, idan kayi mata rantsuwa ko kashedi ba za ta saɓa maka ba, idan ba kanan ko kayi tafiya za ta kiyaye maka dukiyar ka da mutuncin ta.

Idan muka kalli waɗannan hadisai guda uku za mu ga sun zo da siffofi  guda goma sha ɗaya kenan.

Sune: 

1. Mai Addini

2. Mai kuɗi

3. Mai kyau

4. Mai matsayi 

5. Mai soyayya

6. Mai haihuwa

7. Mai faranta rai

8. Mai biyayya

9. Mai ɗaukar tsawa da kashedi

10. Mai kiyaye dukiya

11. Mai kiyaye mutuncin ta.

Daga waɗanan hadisai na Manzon Allah saw muka samo waɗanan siffofin na irin matar da ya kamata mutum ya nema, amma da wuya a sami wacce ta haɗa dukkan waɗannan siffofin.

 Mace mai tarbiyya de itace abin nema , idan ka sami mai tarbiyya ko gama more aure.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post