YANZU-YANZU | WASU YAN BINDIGA SUN SACE WASU MATA 13 A KATSINA

 Wasu ƴan bindiga sun kai hari yankin ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina inda suka yi awon gaba da mata suka yi daji da su.

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar  da faruwan lamarin inda kakakinta Isah Gambo ya ce ƴan bindigar sun buɗe wa motar da matan ke ciki ƙirar Golf wuta da ke kan hanyarsu zuwa banki a Funtua domin karɓar tallafin da suka samu.

Ya ce mata 13 daga garin Maigora ƴan bindigar suka yi daji da su amma daga baya uku daga cikinsu sun gudo.

A cewar rundunar ƴan sandan an kai harin ne ranar Alhamis da safe.

Katsina na cikin jihohin arewa maso yammaci da ke fama da matsalar ƴan fashi masu garkuwa da mutane domin kudin fansa.

A watan Disamba sama da ɗaliban sakandare 300 ƴan bindiga suka sace kafin daga suka sace su.

Wannan kuma na zuwa a yayin da wasu ƴan bindigar suka abka makarantar sakandare a Kagara jihar Neja suka saci dalibai a ranar Laraba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post