Yanzu-Yanzu | Karamar HUKUMAR GUMEL DAKE JIGAWA TA SAUKAKAWA MASU NEMAN AURE

 

YANZU-YANZU | Karamar hukumar Gumel dake jihar Jigawa ta saka doka don sauƙaƙawa masu neman aure faɗin karamar hukumar.


DAGA El farouq Jakada


Karamar hukumar Gumel ta saka wasu dokoki bisa sauƙaƙa wa masu niyyar yin aure, Amma saboda wasu al'adun abin saiya faskara.


Kadan daga cikin dokokin gasu kamar haka:-Haramta biyan kuɗin sadaki fiyeda ƙima

-Haramta kayan na gani inaso

-Haramta kayan gara

-Haramta shagula da yawa irinsu Arabian night da Fulani day, dadai sauransu

-Haramta kaɗe-kaɗe na zamani don rake chakuɗanyar maza da mata

-Haramta hawan Angwanci (batare da izinin masarautar Gumel

-Haramta kayan saka rana

-Takaita lokacin shagali daga 6:am zuwa 6:pm

-Haramta zuwa daukar Amarya da motoci fiyeda kwara ukku

-Takaita kayan lefe(kayan sawa kala 6 sai takalma da ɗan kunne da sarka gami da gyale da hijabi kowanne kala 3 sai kayan kwalliya kala biyu-biyu


Sannan idan mutum ya zabi ba zaiyi lefe ba zai bada kudin wanda bazasu wuce dubu dari, kazalika wanda ya karya wannan doka zai iya samu hukunci na zama gidan gyaran hali na tsawon wata ukku da tarar dubu hamsin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post