IRIN HALIN KUNCIN DA ZAWARAWA SUKE SHIGA YAYIN ZAMAN ZAWARCI


A tattunawar da akayi da wasu zawarawa sun bayyana irin halin da suke shiga na kunci yayin zaman zawarci, 


KARANTA: Idan kasan baka iya yin mintuna 8 kana jima'i ka gaggauta yin wannan hadin

KARANTA: Wasu hanyoyi 8 da zaka kiyaye lafiyar maniyyinka

KARANTA: Wannan shine ake kira hadin yar gata, matan aure zalla


Binciken jaridar Aminiya a Jihar Kano ya gano cewa zawara musamman wadanda iyayensu ba su da karfi suna shiga wani hali na kaka-ni-ka-yi sakamakon canjin rayuwa da sukan samu lokacin da suka dawo gidan iyayensu.


Wannan ya hada da rashin samun isasshen abinci da wurin kwana da sauran abubuwan rayuwa, musamman idan aka rasu aka bar su da yara marayu.


‘Ko wacce muke gaba ba na mata fatan zawarci’


Malama Halima Muhammad, daya ce daga cikin irin wadannan zawarawa wadda ta ce ta kai shekara biyar tana zawarci.


Ta bayyana wa Aminiya cewa a yanzu haka sakamakon halin da ta tsinci kanta a ciki bayan dawowarta gaban iyayenta ta shiga da-nasanin mutuwar aurenta.


“A kullumu ina da-na-sanin mutuwar aurena musamman idan na tuna yadda maigidana yake hidima da ni da ’ya’yana.


“Amma kaddarar mutuwar aure ta shiga tsakaninmu. A yanzu ga shi a gidanmu, ni nake fafutikar abin da zan ci ni da ’ya’yana, domin dan abin da baban yaran ke bayarwa a wata ba isar mu yake ba.


“Babu wanda yake taimaka min, a gidanmu in takaice miki labari daga wanda ake kawo min albarkacin ’ya’yana kannena suke dan samu.


“Abin ba dadi ko kadan, ko wacce muke gaba da ita ba na yi mata fatar zawarci,” inji ta.


‘’Yan uwana sun juya min baya’


Wata bazawara mai suna A’isha Mansur ta ce ta tsinci kanta a halin ni-’ya-su sakamakon juya mata baya da ’yan uwanta suka yi bayan da aurenta ya mutu ta dawo gida.


“Lokacin da na dawo gida ’yan uwana da iyayena ba su goyi bayana ba a kan rigimar da ta shiga tsakanina da mijina har ta kai ga rabuwar aurenmu.


“Saboda haka aka bar ni na zauna a gidan amma ni nake yi wa kaina komai na rayuwa.


“Gaskiya ba zan ce iyayena talakawa ba ne sosai, suna da dan rufin asirinsu amma haka mahaifina ya ki yarda ya dauki nauyina.


“A yanzu haka rayuwata kacokan ta dogara a kan ’yar sana’ar da nake gudanarwa ta awara, a ciki nake yin komai na rayuwata,” inji ta.


Zawarci akwai kawo kaskanci

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post