Yadda Za'a Magance Fitsarin KwanceAssalamu alaikum warahamatullah ta'ala wabarakatuhu. 


Insha Allahu a yau cikin wannan rubutu zakuji hanyoyi daga cikin hanyoyin dake magance fitsarin kwance na manya da yara.

Musamman waɗanda suka fara manyan ta suna fitsarin kwance to za'a iya jarraba masu wannan hanyan insha Allah za'a samu waraka.


Abubuwan da ake bukata sune Kamar haka:


(1) Kankana

(2) Tafarnuwa

(3) Tsamiya

(4) Kurkur

(5) Citta (ɗanya) 


 Idan kun samu wannan abubuwan da muka lissafa a sama, za'a kankare Kurkur ɗin sai a ɓare tafarnuwa ayanka ta, ko kuma a daka sannan ita ma kankana za'a feraye bayanta ita kuma citta za'a yankata ko kuma a daka.


Sai a haɗe su a dafa su sosai su dafu, daga nan bayan an sauke sai a bari ya huce sai ya ɗau lokaci kamar minti 10, sannan sai a tace, ana iya saka zuma kamar cokali haɗu, sai a rinƙa ba wa yaro yana sha kamar cokali 3, sau uku a rana, idan babbane zai riƙa shan a ƙalla kamar girman kofin shayi, sau biyu a rana.


Amma idan ana zargin akwai alamomin jinnu, ko sihiri, musamman idan manyane to bayan an haɗa sai ayi masa ruqiyya domin a haɗa fa'ida biyu.


Allah yasa mu dace amen. 

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post