MAGANIN MAZINACIN ALJANI [NAMIJIN DARE]

 

MAGANIN MAZINACIN ALJANI[NAMIJIN DARE].

               Hanyoyin maganceshi:-

     Zamu ambaci guda biyu insha allah za,a dace da amfani da wadannan hanyoyi sune kamar haka:-

             HANYA TA FARKO:-

   Komawa zuwa ga mahalicci da karatun al-qur'ani:

Da  kuma ruko da addu'o'in da manzon tsira ya bamu:


           [a] na safiya


           [b] da yammaci


           [c] dana shiga bayi


           [d] da fitowa daga bayi


           [e] dana shiga gida


           [f] dana fita


           [g] da na kwanciya barci


           [h] dana tashi


           [i] dana sanya sutura


           [j] da cirewa


           [k] dana cin abinci


        duk wadannan manzon tsira ya koya mana su acikin hadisai ingantattu,sai ki duba littafin:-


                  [HISNUL MUSLIM]  

Sannan kuma sai malamai suka bada wasu hanyoyin guda[11] game da macenda take fama da wannan matsalar ko namijin da yake fama da wannan matsalar sune kamar haka:-


[1]Su rinka kiyaye dokokin ubangiji  da kuma nisantar laifuffuka na sabo


[2]Yawaita karatun Al-qur'ani ako wani hali mutum ya tsinci kansa kuma ko wani lokaci.


[3]Kyautata sutura [mace]take sanya hijabi daga sama har kasa, hijabin kuma mai kauri, sannan mai fadi ba wanda zai matseta ba.


[4]kiyaye cin halal wanda za,aci ko za,a nema.


[5]Yin sallah akan lokaci tare da kiyaye iliminta ayita kamar yadda manzon tsira ya koyar.

[6]Yawan zama da al-wala da kuma idan za,a kwanta barci kullum.


[7]Yawan karanta.


           [Ayatul kursiyyu]


          [Amanarrasulu]


          [Qul-huwallahu]


           [Falaki] 


            [Nasi]


     yayin da za,a kwanta barci.


[8]Yawan karanta Suratul-Bakara acikin gida ko dakin da ake kwana, sannan acire dukkanin wani hoto daga daki.


[9]Yawan karanta [LA'ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU,LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU,WAHUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR].sau 100  safe da yamma.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post