KUSKURE 9 DA MA'AURATA SUKE TAFKAWA


 KUSKURE 9 DA MA'AURATA SUKE TAFKAWA A RAYUWAR SU TA AURE.


Akwai abubuwa da yawa wadanda Ma’aurat suke aikatawa a lokacin Jima’insu.


1. RASHIN GABATAR DA WASANNI KAFIN JIMA’I:*

Wannan ba daidai bane domin kuwa Manzon Allah (saww) yace “IDAN ‘DAYANKU YAYI NUFIN KUSANTAR IYALINSA, TO LALLAI A SAMU ‘DAN AIKE A TSAKANINSU”. Sai Sahabbai suka ce “Wanne irin ‘dan aike?” Sai yace “SHI NE SUMBA (KISS) DA KUMA MUBASHARA (RUNGUMAR JUNA).

 Rashin gabatar da irin wadannan wasannin yakan haifar da rashun gamsuwar Jima’i. Yana daga cikin fa’idodin gabatar da wadannan wasannin, zai sa Maniyyin ita Macen ya gangaro daga ainihin inda yake, sannan kuma za ta samu cikakkiyar gamsuwa.

2. KUSKURE NA BIYU SHI NE TSOTSON AL’AURAR JUNA:

 Sai dai shikuma wan Nan akwai bayanai akansa.

3. KUSKURE NA UKU SHINE YIN SURUTAI A LOKACIN JIMA’I Shi ma 

wannan ba daidai bane. Shari’ar addinin Musulunci ta hana mutum ya rika yin magana a lokacin da yake tsirara.

4. KUSKURE NA HUDU SHI NE RASHIN LULLUBE JUNA DA MAYAFI: 

Shima wannan ba daidai bane. yin hakan ya yi kama da Jima’in dabbobi kenan.

5. RASHIN AMBATON ALLAH KAFIN FARA JIMA’I 

Ya kamata Ma’aurata su kula da yin Bismillah tare da karanta addu’ar nan wacce Manzon Allah (saww) yace duk wanda yake karantawa yayin Jima’i da matarsa, to indai aka samu rabo, to shaitan ba zai iya cutar da yaron ba. Ga addu’ar nan: “BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAITAN WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAQTANA”.

6. Idan Miji ya biya bukatarsa, to bai kamata ya gaggauta sauka ba, har sai ita ma matarsa ta biya bukatarta.


7. RASHIN SAUYA YANAYIN KWANCIYA: 

Shi ma wannan ayar Alqur’ani ta bada damar miji ya sadu da matarsa bisa kowanne irin yanayi. A tsaye ko azaune ko a kwance ko a tsugunne, mutukar dai ba ta dubura bane. Don haka ya halatta Ma’aurata su rika chanza yanayin kwanciyarsu saboda kara ma juna nishadi.


8. SADUWA A LOKACIN DA TAKE CIKIN JININ HAILA, KO JININ HAIHUWA Allah (SWT) ya ce : “KU NISANCI MATA A LOKACIN HAILA. KAR KU KUSANCESU HAR SAI SUNYI TSARKI”.


9. SADUWA TA DUBURA.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post