DILLALAN SHANU DA MASU KAYAN ABINCI SUN FARA YAJIN AIKI SABODA TASHIN HANKALIN DA YAFARU A IBADAN

Dillalan  shanu da kayan abinci karkashin shugabancin kungiyarsu ta kasa AUFCDN  sun fara yajin aiki daga yau Alhamis a fadin Najeriya bayan cikar wa’adin kwanaki bakwai da suka bai wa gwamnatin tarayya na biya musu bukatunsu.

A ranar Lahadi ne Kungiyar AUFCDN wadda ta hade da Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC  ta ce, tana son gwamnati ta bai wa  mambobinta kariya tare da biyan ta diyyar Naira biliyan 475 saboda  kisan da aka yi wa ‘ya’yanta da kuma asarar da ta tafka a lokacin zanga-zangar EndSARS da kuma rikicin kasuwar Shasa da ke garin Ibadan.

Kazalika kungiyar ta bukaci gwamnati da ta bada umarnin janye shingayen binciken ababan hawa da aka kafa a manyan hanyoyin kasar saboda matsalolin da mambobinta ke fuskanta a yayin  gudanar da harkokinsu na jigilar abinci da shanu.

Daya daga cikin jiga-jigan kungiyar ta AUFCDN, Hajiya Hauwa Kabir Usman, ta bayyana cewa, an tanadi jami’an kungiyar da za su tabbatar da cewa, ba a yi jigilar shanu da abinci daga arewaci zuwa kudancin  Najeriya ba a yayin wannan yajin aikin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post