![]() |
| Jami’an Civil Defence Sun Kama Matashi Mai Shigar Mata a Yobe |
Jami’an Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a jihar Yobe State sun kama wani matashi mai suna Kamaluddin Abbas bisa zargin yin shigar mata domin ya rika ziyartar budurwarsa a gidan iyayenta ba tare da an gane shi ba.
Rahotanni daga majiyoyi sun nuna cewa, matashin ya dade yana amfani da wannan dabara, inda a duk lokacin da ya je gidan, iyayen yarinyar ke daukar cewa wata kawar diyarsu ce ta zo ziyara. Wannan ya ba shi damar shiga gida cikin sauki ba tare da wata shakka ba.
An ce har ma ana karɓar sa cikin mutunci da girmamawa, inda ake kawo masa abinci da abin sha kamar yadda ake yi wa baki na gaskiya, alhali ba a san cewa namiji ne ke shigowa cikin kayan mata ba.
Sai dai lamarin ya zo karshe ne bayan jami’an tsaro sun samu bayanai kan abin da ke faruwa, inda suka dauki mataki cikin gaggawa suka kama wanda ake zargin. Hukumar NSCDC ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken yadda aka shirya wannan dabara da kuma daukar matakan doka da suka dace.
Hukumar ta kuma yi kira ga iyaye da su rika kula da irin mutanen da ke ziyartar ‘ya’yansu, tare da tabbatar da sahihancin su, domin kaucewa irin wadannan lamurra da ka iya jawo matsaloli a cikin al’umma.
Wannan lamari ya jawo cece-kuce a tsakanin mazauna yankin, inda mutane da dama ke nuna mamaki kan yadda aka iya aiwatar da irin wannan dabara na tsawon lokaci ba tare da an gano ba.
