ZoyaPatel
Ahmedabad

DA ƊUMI-ƊUMI: Hamisu Breaker Ya Auri Jaruma Hafsat Idris

DA ƊUMI-ƊUMI: Hamisu Breaker Ya Auri Jaruma Hafsat Idris

Hamisu Breaker Ya Auri Jaruma Hafsat Idris 


Rahotanni da ke yawo sun nuna cewa fitaccen mawaƙin Kannywood, Hamisu Breaker, ya shiga sahun masu aure, bayan da ake zargin ya ɗaura aure da shahararriyar jaruma Hafsat Idris, wacce aka fi sani da Ɓarauniya.

An ce ma’auratan sun dade suna hulɗar soyayya a ɓoye, kafin daga bisani suka yanke shawarar kulla aure cikin sirri, lamarin da ke jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masoyansu da masu bibiyar harkokin Kannywood.

Majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da bikin auren ne cikin natsuwa a makon da ya gabata, kodayake har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangarorin biyu domin tabbatar da sahihancin labarin.

Idan har wannan rahoto ya tabbata, Hamisu Breaker da Hafsat Idris za su shiga jerin fitattun jaruman Kannywood da suka rungumi aure a ɓoye a ‘yan kwanakin nan.

Masoya da masu bibiyar harkokin nishadi na ci gaba da tura sakonnin taya murna tare da fatan alheri ga ma’auratan, yayin da ake jiran karin bayani daga gare su.

Me za ku yi musu fatan alheri?


[Related Posts]
Mumbai
Kolkata
Bangalore
Previous Post Next Post