ZoyaPatel
Ahmedabad

Yadda ‎’Yan bindiga suka hallaka mutum 13 a wurin bikin aure a Kaduna

Yadda ‎’Yan bindiga suka hallaka mutum 13 a wurin bikin aure a Kaduna
‎’Yan bindiga suka hallaka mutum 13 a wurin bikin aure a Kaduna 


Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka fada hannun ’yan bindiga, sakamakon wani mummunan hari da aka kai a wurin bikin daurin aure a kauyen Kahir, cikin Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, da misalin karfe 11 na daren Lahadi.



‎Wani mazaunin yankin, Shehu Bala, ya bayyana cewa maharan dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kutsa cikin dakin taron bikin, inda suka bude wuta kan jama’a ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 13 nan take.

‎Ya kara da cewa an yi gaggawar kai wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Kagarko domin samun kulawa, yayin da aka tura mutum biyu da ke cikin mawuyacin hali zuwa Kaduna domin karin jinya.

‎Shehu ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, yana mai cewa, “Abokaina biyu da ke cikin dakin taron sun jikkata. Amma tsananin harbe-harben da aka yi ya hana sanin yawan wadanda aka sace.”

‎Wani shugaban al’umma a yankin ya tabbatar da cewa an yi jana’izar wadanda aka kashe, amma zuwa yanzu ’yan bindigar ba su tuntubi kowa ba dangane da wadanda suka sace.

‎Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shafe kusan awa guda suna barna, inda suka fasa shaguna tare da kwashe kayayyaki da magunguna daga wani kantin sayar da magani.

‎Wata majiya daga rundunar ’yan sanda a Kagarko ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta ce har yanzu ba a tantance yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ba.

‎Hakazalika, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa za a fitar da cikakken bayani nan gaba kadan, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin ceto wadanda aka sace.

‎Rahotanni sun kuma nuna cewa Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe, tare da Sanata Sani Musa, sun ziyarci wadanda harin ya shafa a Babban Asibitin Kagarko domin jajanta musu.

‎Al’ummomi da dama a yankin, ciki har da Janjala, sun dade suna fama da hare-haren ’yan bindiga. Kimanin makonni uku da suka gabata, an sace mutane 14, ciki har da wani dan banga da matarsa, wadanda har yanzu suna hannun masu garkuwa da su da ke neman Naira miliyan 14 a matsayin kudin fansa kafin a sake su.


[Related Posts]
Mumbai
Kolkata
Bangalore
Previous Post Next Post