ZoyaPatel
Ahmedabad

Yadda ake gyara wayar da bata rike caji

Yadda ake gyara wayar da bata rike caji
Yadda ake gyara wayar da bata rike caji 



Wayar Android da bata rike caji na daga cikin matsalolin da suka fi damun masu amfani da waya. Kana iya cika caji amma bayan dan lokaci kadan sai caji ya kare, ko kuma wayar zata kashe ko da caji yana nuna kashi mai yawa. Wannan matsala tana yawan faruwa ga wayoyi irin su Infinix, Tecno, Samsung da sauran Android.

A wannan rubutun, za mu yi bayani dalla-dalla kan manyan dalilan da yasa waya bata rike caji, tare da hanyoyin gyarawa masu tasiri da zaka iya gwadawa kafin ka yanke hukuncin canza baturi ko kai waya wurin technician(mai gyara) .

1. Baturi ya tsufa ko ya lalace

Babban dalili mafi yawa shi ne lalacewar baturi. Duk baturin Android na da iyakar rayuwa, kuma bayan dogon amfani:

  • Baturi zai fara sauke caji da sauri
  • Wayar zata kashe kafin caji ya kare
  • Caji baya dawwama koda ba a amfani da waya sosai ba

Idan wayarka ta wuce shekara 2 ana amfani da ita, akwai yiwuwar baturi ne ke da matsala.

2. Apps masu cin caji a baya (Background apps)

Wasu apps na aiki a boye suna cin caji ba tare da sani ba. Wadannan apps na iya:

  • Rage caji cikin sauri
  • Sa wayar ta yi zafi
  • Haddasa battery draining

A AndroidPols.com.ng mun taba yin bayani kan abubuwan da ke cin caji a boye a wayar Android.

3. Wayar na yin zafi sosai

Zafi yana daga cikin manyan abubuwan da ke rage lafiyar baturi. Idan wayar na yin zafi:

  • Baturi na sauke caji da sauri
  • Rayuwar baturi na raguwa

Wannan yana da alaƙa da rubutunmu na dalilin da yasa wayar Android ke zafi sosai.

4. Charger ko cable mara kyau

Amfani da:

  • Fake charger
  • Cable da ya lalace
  • Charger da bai dace da waya ba

na iya sa baturi baya cika caji yadda ya kamata, wanda ke sa ya sauke da wuri.

5. Cikakken storage ko RAM

Idan storage ko RAM ya cika:

  • System na wahala
  • CPU na aiki fiye da kima
  • Wannan na cin caji sosai

6. Matsalar system ko update error

Wasu lokuta bayan system update:

  • Battery usage na iya rikicewa
  • Wayar zata fara sauke caji da sauri

Wannan na faruwa ne idan update bai daidaita da wayar ba.

7. Network ko signal problem

Idan wayar na wahala wajen samun network:

  • Radio na aiki sosai
  • Wannan na cin caji da sauri

Musamman idan kana a wurin da signal baya da kyau.

Hanyoyin gyara wayar da bata rike caji

1. Duba battery usage

  • Shiga Settings > Battery
  • Ka duba apps da ke cin caji fiye da kima
  • Ka goge ko ka rage amfani da su

2. Rufe background apps

  • Ka kashe apps da basa bukata
  • Ka hana wasu apps yin aiki a baya

3. Rage zafi

  • Guji amfani da waya yayin caji
  • Kada ka bar waya a rana
  • Rage wasanni masu nauyi

4. Yi amfani da original charger

  • Ka guji fake charger
  • Ka tabbata charger ya dace da wayarka

5. Goge apps marasa amfani

  • Ka cire apps da baka amfani da su
  • Wannan na rage load ga system

6. Share cache

  • Ka goge cache na apps
  • Ko ka yi wipe cache partition ta recovery mode

7. Sabunta Android

  • Duba ko akwai system update
  • Sabuntawa na iya gyara battery draining

8. Factory reset (idan ya zama dole)

Idan komai ya kasa:

  • Ka yi factory reset
  • Ka tabbata ka ajiye bayananka

Lokacin da ya dace a canza baturi

  • Idan wayar na sauke caji cikin mintuna
  • Idan tana kashewa a kashi 30–40%
  • Idan baturi na kumbura ko yana yin zafi

A wannan hali, canza baturi shine mafita mafi kyau.

Kammalawa

Wayar Android da bata rike caji na iya kasancewa sakamakon lalacewar baturi, apps masu cin caji, zafi, charger mara kyau, ko matsalar system. Idan aka bi hanyoyin da ke sama, yawanci matsalar zata ragu ko ta tafi gaba ɗaya.

Domin samun ingantattun Android Hausa tutorials masu warware matsaloli kai tsaye, ka rika ziyartar AndroidPols.com.ng, inda ake kawo bayanai masu amfani cikin Hausa mai sauƙin fahimta.


[Related Posts]
Mumbai
Kolkata
Bangalore
Previous Post Next Post