![]() |
| Wayar Android tana makale a logo, yaya ake gyara |
Idan wayar Android tana makale a logo (wato tana nuna alamar kamfani kamar Infinix, Tecno, Samsung ko Android kawai amma bata wuce nan ba), wannan matsala tana nufin system bai kammala kunnawa ba. Wani lokaci wayar zata tsaya a logo na dogon lokaci, wani lokaci kuma zata rika restarting amma bata shiga home screen.
Wannan matsala tana kama da bootloop, kuma tana daga cikin matsalolin system errors da suka fi yawa a wayoyin Android.
A wannan rubutun, za mu yi bayani dalla-dalla kan dalilan da ke sa waya ta makale a logo, sannan mu nuna hanyoyin gyara masu aiki da zaka iya gwadawa kafin kai waya wurin technician(gyara).
Dalilan da yasa wayar Android ke makale a logo
1. System update da bai kammala ba
Idan kana sabunta Android sai:
- Caji ya ƙare
- Aka katse update
- Wayar ta kashe yayin update
to system files na iya lalacewa, wanda hakan ke sa wayar ta makale a logo.
2. Android system error
Wasu kurakuran system na iya faruwa sakamakon:
- Shigar da app mara kyau
- Virus ko malware
- System crash
Wannan yana hana Android kammala booting.
3. Cikakken storage
Idan memory na waya ya cika sosai:
- Android na kasa loading
- Wayar zata tsaya a logo
Wannan na yawan faruwa a wayoyi masu ƙaramin storage.
4. Bootloop da ke da alaƙa da apps
Idan ka shigar da wani app kwanan nan, musamman daga waje (APK), yana iya rikicewa da system har ya sa waya ta makale a logo.
Mun yi bayani dalla-dalla kan yadda ake gyara wayar da ta makale a bootloop a AndroidPols.com.ng.
5. Matsalar hardware
Idan wayar:
- Ta fadi sosai
- Ta jiku da ruwa
- Ta yi zafi fiye da kima
to motherboard ko baturi na iya samun matsala, wanda ke hana waya wucewa daga logo.
Hanyoyin gyara wayar Android da ta makale a logo
1. Jira na ƴan mintuna
Wani lokaci wayar na iya ɗaukar lokaci:
- Musamman bayan system update
Ka jira mintuna 5–10 kafin ka yanke hukunci.
2. Force restart
Wannan shi ne mataki mafi sauƙi:
- Riƙe Power button na sakan 20–30
- Idan bai yi aiki ba, riƙe Power + Volume Down
Wannan yana tilasta wayar ta sake farawa.
3. Shiga Recovery Mode
Idan force restart bai yi aiki ba:
- Kashe waya gaba ɗaya
- Riƙe Power + Volume Up (ko Volume Down a wasu wayoyi)
- Jira har Recovery Mode ya bayyana
4. Wipe cache partition
A cikin Recovery Mode:
- Zaɓi Wipe cache partition
- Ka tabbatar
- Sannan ka zaɓi Reboot system now
Wannan baya goge data amma yana share files masu haddasa matsala.
5. Factory reset (idan babu mafita)
Idan har yanzu wayar tana makale a logo:
- A Recovery Mode, zaɓi Wipe data/factory reset
- Ka tabbatar
Lura: Wannan zai goge dukkan bayanai (apps, hotuna, files).
6. Flashing original firmware
Idan factory reset bai yi aiki ba:
- Ana bukatar a sake saka original firmware
- Wannan yana bukatar PC da ƙwarewa
Idan baka da ilimi sosai, kada ka gwada da kanka.
Lokacin da ya dace a kai waya wurin technician(gyara)
- Idan wayar bata wuce logo ko kaɗan
- Idan babu alamar caji
- Idan matsalar ta fara bayan shiga ruwa
- Idan flashing ko reset bai yi aiki ba
A wannan hali, matsalar na iya zama hardware, ba software ba.
Yadda zaka kare wayarka daga makalewa a logo
- Kada ka katse system update
- Guji shigar da apps daga waje
- Kada ka bari storage ya cika
- Yi amfani da original charger
- Ka kula da zafin waya
Kammalawa
Wayar Android da ke makale a logo ba lallai tana nufin ta lalace gaba ɗaya ba. A mafi yawan lokuta, system error, update problem, ko app issue ne ke haddasa hakan, kuma ana iya gyarawa ta hanyar recovery mode ko factory reset.
Domin karin Android Hausa tutorials masu inganci da warware matsaloli, ka rika ziyartar AndroidPols.com.ng, inda ake kawo bayanai masu amfani cikin Hausa mai sauƙin fahimta.
