ZoyaPatel
Ahmedabad

Dalilin da yasa wayar Android bata kunna wa — Android Pols

Dalilin da yasa wayar Android bata kunna wa
Dalilin da yasa wayar Android bata kunna 


Wayar Android bata kunna wa ba matsala ce da mutane da yawa ke fuskanta ba, musamman masu amfani da Infinix, Tecno, Samsung da sauran wayoyin Android. Wani lokaci wayar zata daina kunnawa kwatsam, wani lokaci kuma zata nuna alama amma ta ƙi tashi gaba ɗaya. Wannan matsalar na iya jawo damuwa sosai, musamman idan wayar na ɗauke da muhimman bayanai.

A wannan rubutun, za mu yi bayani dalla-dalla kan manyan dalilan da yasa wayar Android bata kunna, da kuma hanyoyin gyarawa masu sauƙi kafin ka kai ta wurin technician(mai gyara) .

1. Caji ya ƙare gaba ɗaya (Deep Battery Drain)

Daya daga cikin manyan dalilai shi ne cajin baturi ya ƙare gaba ɗaya. Idan ka bar waya bata da caji na dogon lokaci, baturin na iya shiga yanayin da ake kira deep discharge, wanda ke hana wayar kunnawa nan take.

Abin da zaka yi:

  • Ka saka waya a caji na akalla mintuna 30 zuwa awa 1
  • Kada ka yi ƙoƙarin kunnawa nan take
  • Ka tabbatar kana amfani da original charger

A wasu lokuta, bayan caji mai tsawo, wayar zata kunna lafiya.

2. Charger ko USB ya lalace

Wasu lokuta ba wayar bace matsala, charger ko cable ne ya lalace. Wannan yana sa ka yi tunanin wayar bata kunna wa alhali kuwa bata samun wutar caji.

Yadda zaka tabbatar:

  • Ka gwada wani charger daban
  • Ka gwada saka waya a caji a wani socket
  • Ka lura ko alamar caji tana bayyana ko a’a

A AndroidPols.com.ng mun taba yin bayani kan dalilin da yasa wayar bata karɓar caji, wanda shima na da alaƙa da wannan matsalar.

3. Wayar ta daskare (System Freeze)

Wani lokaci wayar na iya daskarewa gaba ɗaya, har ta kasa amsa umarnin kunnawa. Wannan yakan faru idan system ya yi overload ko wani app ya lalata tsarin Android.

Hanyar gyara:

  • Ka riƙe Power button na tsawon sakan 15–30
  • Idan bata kunna ba, ka riƙe Power + Volume Down tare

Wannan hanya na taimakawa wajen tilasta wayar ta sake farawa.

4. System Error ko Android Crash

Idan Android system ya samu matsala, wayar na iya ƙin kunnawa gaba ɗaya. Sau da yawa ana samun wannan matsala bayan:

  • Sabunta Android (system update)
  • Shigar da app mara kyau
  • Virus ko malware

A irin wannan hali, wayar zata iya makale a logo ko kuma ta mutu gaba ɗaya.

Abin da za a yi:

  • Gwada shiga Recovery Mode
  • Yi restart ko wipe cache partition idan akwai

Mun yi karin bayani kan irin wannan matsala a rubutun Android system errors da hanyoyin gyarawa a AndroidPols.com.ng.

5. Power Button ya lalace

Idan power button ya lalace ko ya makale, wayar bazata kunna ba koda tana da caji. Wannan na faruwa ne sakamakon:

  • Faduwar waya
  • Shiga ruwa
  • Dogon amfani

Alamomin wannan matsala:

  • Babu wani response idan ka danna power
  • Wayar na iya nuna caji amma bata kunnawa

A irin wannan hali, ana bukatar gyaran hardware.

6. Shiga Ruwa ko Danshi

Idan waya ta taɓa ruwa ko danshi, yana iya lalata internal components, wanda hakan ke hana ta kunnawa.

Idan hakan ta faru:

  • Kada ka yi ƙoƙarin kunnawa
  • Kada ka saka a caji
  • Ka kai ta wajen gyara da wuri

Jinkiri na iya ƙara lalata wayar.

7. Baturi ya lalace

Idan wayar ta dade ana amfani da ita, baturin na iya lalacewa. Idan baturi ya lalace:

  • Wayar bazata rike caji
  • Zata kashe ko ƙi kunnawa gaba ɗaya

Wannan matsala tana yawan faruwa ga wayoyin da suka wuce shekara 2–3 ana amfani da su.

8. Motherboard ko IC problem

Wannan shi ne mafi tsanani daga cikin dalilan. Idan motherboard ya samu matsala:

  • Wayar bata kunna ko kaɗan
  • Babu alamar caji
  • Wani lokaci zafi na iya fitowa

A wannan mataki, sai kwarren technician(Mai gyaran waya) ya duba wayar.

Abubuwan da zaka gwada kafin kai waya gyara

  • Gwada wani charger
  • Saka waya a caji na tsawon lokaci
  • Yi force restart
  • Duba ko waya ta taba ruwa
  • Ka tuna ko ka yi system update kwanan nan

Yawancin matsalolin nan ana iya magance su ba tare da kashe kudi mai yawa ba.

Kammalawa

Dalilan da yasa wayar Android bata kunna wa suna da yawa, daga matsalar caji, system error, har zuwa lalacewar hardware. Abu mafi muhimmanci shi ne ka fara da sauƙaƙan hanyoyin gyara kafin ka yanke hukuncin kai waya gyara.

Idan kana son karin irin wannan Android Hausa tutorials masu inganci, zaka same su a AndroidPols.com.ng, inda ake warware matsalolin Android dalla-dalla cikin Hausa mai sauƙin fahimta.

[Related Posts]
Mumbai
Kolkata
Bangalore
Previous Post Next Post