![]() |
| BAYANI AKAN MACE HARIJA: Fahimtar Halitta Da Jikin Mace |
A cikin jerin halittun da Allah (SWT) ya halitta, akwai bambance-bambance da dama a tsakanin mata, musamman wajen sha’awa da jin daɗin saduwa. Daya daga cikin wannan irin halayyar mace ita ce wanda ake kira HARIJA. Wannan kalma na nuni da wata mace musamman mai irin tsarin sha’awa da jiki, wadda ba a iya haɗa ta da mace irin kowa ba.
1. MENENE HARIJA?
Harija ba wai mace ce mai yawan sha’awa ba, a’a, mai ƙarfi ce wajen jurewa sha’awa da jurewa lokacin saduwa. Ma’ana, tana iya jimawa a lokacin jima’i ba tare da ta kawo (releasing) ba. Wannan na nufin cewa akwai tsawon lokacin da ake bukata domin ta kai kololuwa. Ta na buƙatar natsuwa, kuzari, da cikakkiyar fahimta daga mijinta.
2. ME YAKE SA mace HARIJA Take DADEWA bata KAWO ba?
Wannan na da alaka da tsarin halittar farjinta da yadda jikinta ke aiki. Yawanci fanfon gamsuwarta yana da zurfi sosai – yana da nisa fiye da na sauran mata da dama. Don haka:
Sai an zurfafa saduwa sosai kafin a iya taɓa fanfon gamsuwarta.
Ba kowane namiji ba ne zai iya kaiwa wannan zurfin ba.
Wannan yasa, har sai an jima da ita sosai sannan take jin gamsuwa.
Wannan yana sa namiji ya wahala idan bai fahimta ba, ko bai da kuzarin da zai iya jurewa hakan.
3. HALAYYEN MACE HARIJA
Wasu daga cikin alamomin mace Harija suna bayyana a zahiri, ko da ba tare da an yi saduwa da ita ba. Ga wasu daga ciki:
Mace siririya: Yawancin Harijoji sukan kasance sirara, su na da siffa mai laushi da sauƙin motsa jiki.
Dogon wuya: Yawan dogon wuya yana nuni da tsarin jijiyoyi da tsokoki masu jurewa sha’awa da jan lokaci.
Yatsar kafa ta biyu tafi ta farko tsawo: Wannan wani alamar halittar jikinta ne da wasu masana suka alakanta da karfin sha’awa ko gamsuwa mai zurfi.
Dogon numfashi ko yawan jinkirin daukar numfashi yayin motsi: Wannan na nuni da jurewa ci gaba da motsa jiki ba tare da gajiya ba.
HARIJAr mace DA RAYUWAR AURE
Harija tana iya zama mace mai tsananin haƙuri da jinkiri a rayuwa, amma idan lokacin saduwa ya yi, tana buƙatar cikakken ƙoƙari daga mijinta. Wannan yana nufin cewa:
Ba kasafai take buƙatar jima’i ba — zata iya shafe makonni ko watanni ba tare da ta damu ba.
Amma idan lokacin ya yi, ta fi kowa ƙarfin buƙata da nisa a gamsuwa.
Misali: Namiji zai iya yin kusan awa guda yana kokari kafin ya ji tana shiga cikin nutsuwar saduwa. Wannan ba saboda ta daɗe ba ne, sai saboda tsarin jikinta na buƙatar zurfi da ƙwazo.
SHAWARA GA MAZA
Idan ka ga matarka tana da irin waɗannan halaye, kada ka ɗauka cewa ba ta jin daɗin saduwa da kai, ko tana ƙin jima’i da kai. A’a! Wata kila Harija ce.
Ka koyi sabbin hanyoyin jima’i da salo na romantic touch, slow pace, da nutsuwa.
Ka guji fushi ko haushin rashin kawowarta da wuri.
Harija tana buƙatar namiji mai haƙuri da fahimta – ba wadda zata bi kowanne irin salo ba.
A KARSHE: KADA A FAHIMCI HARIJA DA LAIFI
Wasu maza suna zargin mata irin HARIJA da rashin jin daɗi mu'amala. A’a! Wannan rashin fahimta ne. Su ma sun fi buƙatar kulawa da fahimta fiye da wasu mata. Domin:
Sha’awarsu tana da zurfi, amma ba ta fitowa sau da yawa.
Gamsuwarsu tana buƙatar lokaci da ƙwazo.
Suna jin daɗin saduwa, amma sukan danne saboda suna jin mazan ba za su iya jure hakan ba.
Mata Harijoji na da daraja, ba laifi bane kasancewa Harija – amma buƙatar ilimi ne da fahimta daga duka ma’aurata.
