Majalisar dokokin Kano ta yi wa dokar tace fina-finai garambawul
|  | 
| Abba El-Mustapha | 
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da yi wa dokar da ta kafa hukumar tace fina-finai wani babban gyaran fuska. Wannan gyaran ya ƙunshi ƙarin ƙa’idoji da takunkumi, gami da tilasta wa wuraren da ake gudanar da bukukuwa da taruka (event centres) yin rajista a hukumar.
Ayyukan hukumar tace fina-finai suna da muhimmanci musamman a arewacin Najeriya, saboda rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin hukumar da masu shirya fina-finai. Saboda haka, majalisar ta yi wa dokar da aka kafa tun shekara ta 2001 wani babban gyara, domin dacewa da sauye-sauyen da suka faru a fagen shirya fina-finai. Majalisar ta bayyana cewa dole ne a sanya ƙarin birki a wasu abubuwa don kare addini da al’adun jihar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Husaini Dala, ya bayyana cewa, "Yanzu hukumar ta kara samun iko a kan abubuwa da dama." Ya kara da cewa, daga yanzu babu wanda zai shigo birnin Kano ya yi ta ɗaukar fim ba tare da samun izinin hukumar ba.
A wani ɓangare, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya yi kira ga masu wallafa bidiyo a kafofin sada zumunta (content creators) da su guji duk wani abu da zai saba wa mutuncin addini ko al’adun Bahaushe da al’ummar jihar Kano. Ya ce, "Za su mara wa waɗanda ke bidiyo don nishaɗi ko samun arziki, amma ba zagin mutane ba."
Bugu da ƙari, El-Mustapha ya ce masu amfani da kafofin sada zumunta su sani cewa hukumar tana da hurumi kan duk wani abu da ya saba wa addini da al’adu. Ya ce, muddin aka samu korafi game da wani bidiyo ko abu da aka saka a shafukan sada zumunta, hukumar za ta ɗauki matakin da ya dace.
Bayanai sun nuna cewa majalisar dokokin jihar Kano ta kammala aikin gyaran dokar, kuma abin da ya rage shi ne gwamnan jihar ya sanya hannu kan dokar. Duk da haka, babu tabbas ko yaushe ne gwamna zai yi hakan.

 
 
 
 
 
 
 
