| Ingantaccen Maganin Sanyin Mara Na Maza Da Mata |
Barkanmu da saduwa da ku a wannan lokacin a cikin shirye-shirye mu na maganin gargajiya da muke kawo muku, wanda a yau muka kawo muku maganin sanyi wanda maza da mata duk za su iya yin amfani dashi domin a samu wataraka cikin ƙaramin lokaci domin shi wannan haɗin na musamman ne.
Kamar yadda muka saba kawo muku magunguna to yau ma ga wani haɗin, amma shi wannan na musamman ne domin ya bambanta da irin wanda muke kawo muku a baya. Kuma kamar yadda muka ce shi wannan maganin kowa zai iya haɗawa yai amfani dashi. Amma kafin mu faɗa muku yadda ake haɗa maganin yana da kayi ku fara sanin irin alamun da ake ji idan mutun ya kamu da ciwon sanyi.
Kusan kowa da irin alamun da yake ji idan ya kamu da ciwon sanyi wani yadda zai ji ba llale ne wani hakan zaiji ba, wani ma kuma idan ma ya kamu da ciwon sanyin ba zaiji komai ba. Amma dai ga wasu daga cikin alamun da mutum zaiji idan yana da ciwon sanyi Kamar haka;
(1) Idan mace ce za ta ji fitar farin Ruwa daga gaban ta, ruwan yakan zuwa fari kuma mai yauƙi Sannan kuma yanda wari.
(2) Akwai ɗaukewar sha'awa, shi ma yana daga cikin alamun cewa ciwon sanyi ya kama mutum.
(3) Fitowar ƙuraje a gaban mace ko namiji, idan mutum yaga ƙuraje suna feso masa daga gaban sa ko mace ko namiji to shima alama ce dake nuna cewa mutum yana da ciwon sanyi
(4) Saurin inzali, idan kaga yadda kake yin inzali ya canja ba Kamar yadda ka saba yi a baya ba to hakan na nuna cewa sanyi ya kama ka.
(5) Ciwon Idanun, akwai wanda ciwon sanyi kashe musu idanu yake yi, don haka kar mutum yai sake idan yaji idon sa yana yi masa ciwo.
(6) Fitowar ƙuraje a baki da maƙogwaro, shima wasu alamu ne da ke nuna cewa sanyi na damun mutum.
Wannan sune kaɗan daga cikin alamun da mutum zai ji idan ya kamu da cutar sanyi, don haka idan mutum yaji wannan alamun kada ya zauna ya zuba ido.
Amma masu maganin gargajiya duk suna da irin sunan da suke kiran su amma dai duk ɗaya ne kuma haka ake kiran su wato sanyin mara. Amma a ilimin zamani na likitanci suna da sunayen su daban-daban.
Domin magance wannan cuta ta sanyi ku samu wannan abubuwan da za mu ambata kamar haka;
(1) kaninfari, garin sa za'a samu idan kuma babu garin zaku iya yin amfani dashi a haka.
(2) Tafarnuwa, wacce a turance ake kiran ta da garlic ita ma sai a daka ta.
(3) Sai kuma ganyen garafuni, indai kunje wajen masu sayar da ganyen magani da kunce ganyen garafuni kuke so zasu baku.
Idan kun samu wannan abubuwan guda 3 da muka ambata, za ku ɗauko ganyen garafuni din kamar cikin tafin hannu, ko kuma ganyen kamar guda 10. Sai kuma a ɗebi kaninfari kamar cokali 1, sannan ita ma tafarnuwa kamar guda 8 ko 10 sai ku haɗe su waje guda sannan ku zuba ruwa kamar kofi 5 wato Liter 3 sai ku ɗora a kan wuta ku tafasa na tsawon minti 20 ko 30.
Idan ya tafasa sai a sauke tace ruwan a samu mazubi mai kyau a zuba a ciki a saka firinji ya ɗan yi sanyi. Za'a ringa shan kofi ɗaya da safe sannan da dare kafin a kwanta shi ma za'a sha kofi ɗaya. Kuma shi wannan haɗin ana so miji da mata su ringa shan sa domin zai yi musu maganin sanyin dake damun su.
Wannan haɗin ana so ayi amfani dashi har tsawon sati 3 zuwa 4, Insha Allah duk matsalar sanyi da ke damun mutum za'a samu sauƙi. Kuma indai kinsan kina da aure to kiyi ke da mijin ki ku ringa sha, domin idan ke kaɗai kike sha kodai zai yi miki naganin to ba lallai ki samu waraka ba saboda shi mijin ki idan yana da ciwon sanyin zai iya dawo miki dashi. Shi yasa ake so kuyi amfani dashi tare.