Halayen Nagartaccen Namiji A Wajen Mace — Android Pols
![]() |
Halayen Nagartaccen Namiji A Wajen Mace |
Shin ko kunsan halayen da ake iya gane nagartaccen namiji? NAGARTACCEN NAMIJI AGAREKI SHINE MIJI
1. Shine wanda kafin kuyi aure zai damu da ilimin ki da tarbiyar ki da taimaka miki wurin kare mutuncin ki.
2. Wanda zai kira ki da asuba yaji shin kin yi sallah kuwa, kuma ya kira ki da daddare yace kada fa ki kwanta sai kinyi addu'a.
3. Wanda zai aure ki domin tarbiya/halin ki ba domin jikin ki ba.
4. Wanda zai yi fushi dake akan saɓawa Allah da ManzonSa.
5. Wanda ke burin ganin kin zama mace ta gari a gidan mijin, ba wai ki zama mace ta gari a idon duniya ba.
6. Wanda zai kare haqqin ki ya gamsar dake da halal a sama da qasa.
7. Wanda ya fifita dokar Allah da Manzonsa akan jindadin ko ɓacin ranki.
Wallahi a wannan zamanin, samun miji wanda ya damu da addinin ki, ba qaramin sa'a bane, domin mafi yawan maza sun fi damuwa da jikin mace, wanda hakan yasa mata suka fi damuwa da magungunan gyaran jiki akan gyaran tarbiyar su.
Ki gyara tarbiyar ki kafin jikin ki
Ki nemi Miji ba masoyi ba
Ki damu da ilimin Addini fiye da ilimin boko, ki fifita gidan miji akan ki
Allah Ubangiji Yacigaba d hadamu d Masoyan mu n gsky Yakuma Bamu Ikon Ciyar Dasu Tufa Tardasu T Hanyar Halal Yakuma Bamu Ikon Riqe Amanar Dazamu Dauka Har Karshen Rayuwar mu
Amen yahayyu yaqayyum.
بليامن بن أبوبكر
Leave Comments
Post a Comment