Yarinya yar shekara biyu ta rasa ranta sakamakon fyade a Bauchi
![]() |
Yarinya yar shekara biyu ta rasa ranta sakamakon fyade a Bauchi |
Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta bayyana cewa, an yi wa wata yarinya ’yar shekara biyu fyaÉ—e har lahira a Ƙaramar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.
Shafin Aminiya ya rawaito cewa, Jami’in HulÉ—a da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil a wata sanarwa da ya raba wa manemalabarai a ranar Talata, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Nuwamban 2024.
Ya ce, an kai rahoton aikata laifin ne a hedikwatar ‘yan sanda ta Ningi. “An gano gawar wata jaririya a wani masallaci da ke kan titin Deneva, a Ƙaramar Hukumar Ningi da alamun fyaÉ—e aka yi mata,” in ji shi.
“Bayan samun rahoton an aika jami’an tsaro zuwa wurin, inda suka É—auko gawar kuma zuwa babban asibitin Ningi, inda rahoton likita ya tabbatar da cewa jaririyar ta samu munanan raunuka sakamakon kutsawa da aka yi cikin farjinta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.”
Kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Musa Mohammed ya yi Allah-wadai da lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin rashin tausayi da imani.
Wakilin na Aminiya ya bayyana cewa, Kwamishinan ’yan sandan ya umarci jami’in ’yan sandan da ke kula da shiyyar Ningi da su yi Æ™oÆ™arin kamo waÉ—anda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban Æ™uliya.
Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kulawa da su tabbatar da tsaron ’ya’yansu, kar su bari su riÆ™a yawo a kan tituna.
Kakakin ya Æ™ara da cewa, “Rundunar tana neman taimakon jama’a da duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen kamawa da hukunta waÉ—anda suka aikata laifin.”
Leave Comments
Post a Comment