Bello Turji |
Ana rade-radin cewa jami'an tsaron Nijeriya sun yi nasarar kashe dan ta'adda Bello Turji a jihar Sokoto a daren Talata.
Mazauna yankin Sabon Birni suna zargjn Bello ya mutu ne tun bayan wani kofar rago da jami'an tsaro suka yi masa a ranar Asabar din da ta gabata.
Tuni dai wasu mazauna yankunan da lamarin ya auku suka soma yada labarin a shafukan su na twitter.
Jama'a da dama ne ke ta bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin inda mafi Yawan su ke fatan Allah ya tabbatar da wannan labarin.
Daga Ishaka Usman Wali