Abubuwa 10 Dake Sa Maza Gudun Mata Bayan Sunyi kwanciyar Jima'i Da Su

Abubuwa 10 Dake Sa Maza Gudun Mata Bayan Sunyi kwanciyar Jima'i Da Su
Abubuwa 10 Dake Sa Maza Gudun Mata Bayan Sunyi kwanciyar Jima'i Da Su 


Idan aka kasa matan da suka soma yin jima'i kafin su yi aure, kashi 10 ana iya samun kashi 3 ne kawai da suka yi sa'ar auren waɗannan da suka soma lalata dasu. Hakan kuwa yana faruwa ne saboda wasu matan waɗanda ke fara lalatar dasu ko dai 'yan uwansu na jini ne da babu aure a tsakaninsu. Ko kuma waɗannan basu isa aure ba ko dai irin tsoffin nan ne da suke yiwa yara kanana wayo su ribacesu har dai su yi lalata su.


Duk da haka ana samun matan da mazan da suke soyayyar aure dasu ne ke fara yin zina dasu. Hakan kuma yana faruwa ne saboda yadda wasu yan matan suna tunanin idan suka hanawa mai son su da aure kansu yana iya ƙin aurensu. Wasu matan kuma suna gudun ɓacin ran samarin nasu ne suke basu kansu.


Sai dai wani abun baƙin ciki shine da zaran wannan saurayin ya gama lalata budurwar tasa wacce da farko da gaske yake Sonta, sai kuma ya kaurace mata da tunanin cewa ta zama 'yar iska abun da ya koya mata ta na yi da wasu. Ya kasa samun natsuwa da ita har dai sai sun rabu. Daga bisani wanda bashi ya soma buda taba shine zai aureta. Wannan haka yake ga yan mata da dama.


Sai dai a irin wancan lamarin ana samun karancin shekaru ne ga samarin da suke gudun macen da suka soma lalata wa. Shi yasa basa auren su.


Akwai kuma mazan da ba sune suka fara lalata macen ba kuma sun zo da niyar aurenta amma da zaran sun dandana ta sai kuma su kauce kuma su fasa niyar auren ta da suke dashi.


Irin waɗannan mazan ba suna gudun macen bane saboda zina da suka yi da ita, sai dai saboda wasu abubuwan da muka gano su kamar haka. 


1: Dabi'a: Da akawai wasu mazan, duk irin son da suke miki, duk hidimar da zasu miki, suna kwanciya dake sau daya kin fita musu a rai. Bazaki sake ganinsu ba ko sake samun wata damar yin jima'i dasu.


Ba a harkar zina ba kadai, da akwai irin wadannnan maza a cikin mazan aure, wanda da zaran sun auri mace suna kwanciya da ita daga nan ko dai saki ya biyo baya bayan wani lokaci ko kuma tayi ta zama a haka babu jima'i. Irin wadannan mazan sune ake yawan ganinsu suna aure su saka wanda masu iya magana ke kiransu da suna 'auri saki' ko masu auren dandano.


Maza masu irin wannan dabi'ar babu yadda kika iya dasu illa idan kinyi kuskuren fadawa tarkonsu sai ki dauki darasin kare kanki nan gaba.


2: Sana'a Ko Aiki: Akwai wasu mazan da yanayin aikinsu ko sana'arsu na kyamar barin wani ya kusancesu domin gudun kada ya san halin da suke ciki, irin wadannan mazan basu cika son yi soyayya ba, idan suka yi sha'awar mace kuma suka sameta yanada matukar wahala su sake kulata saboda gudun janta a jikin harma tasan halin da yake ciki. Masu wannan dabi'an sunfi yiwa mata na waje musamman matan bariki. Don haka ba abun mamaki bane daga yi sau daya bazaki sake ganinsa ba.


3: Sirri: Mazan dake neman mata a waje suna bukatan sirri, ko dai domin matsayinsu cikin al'uma ko kuma domin boye abunda yake yi wanda yasan ba mai kyau bane.


Irin wadannan mazan idan suka fahimci macen da suka dauko mai surutu ce, wacce zata iya zuwa ta fadawa duniya tsakaninsu to suna afka mata na wannan lokacin bazata sake ganinsa ba barema ta sake samun damar yin wani mu'amala dashi.


4: Tsafta: Maza da yawa ma'aurata, 'yan bariki da masoya suna gujewa matansu bayan sun sadu dasu sau daya. Matan aure kazamai dai duk da wani lokacin mazan na bude idanuwa suci kar su mutu, basa samun gamsuwa irin na jima'i da ya kamata su samu daga wajen mazajensu. Su kuwa wadanda babu lalle babu dole ana samunsu da kazanta shi kenan baki sake ganinsa.


5: Bukatu: Wasu mazan na bariki dana soyayya suna gudun macen da take yawan bijiro da bukatun da suke da yawa ko kuma suka fi karfinsu, don haka zai yi likimo yana lallabaki duk randa ya samu ya afkamiki sai dai ya barki da missed calls. Kiyi ta mamaki irin yadda yake miki hidima a baya amma gashi daga bashi ya daina kulaki. Fahimta yayi bakida wadatar zuci idan ya ci gaba da hulda dake zai galabaita.


6: Matsayinku A Jima'ince: Wannan matsalar yana faruwa ga matan aure dana waje. Idan namiji ya fahimci a farkon yin jima'i kinfi karfinsa ko yafi karfinki da wuya ki sake ganinsa. Idan mai son yin jima'i ne sosai ke kuma bakiso ko kina son shi kuma bayaso to zai iya guduwa ko da kuwa aurenki yake yi.


7: Garkuwa; Wasu matan burinsu su yi jima'i da na miji ne domin samun wani garkuwa daga gareshi. Idan matan aurece burinta tayi ciki ta haifi namiji shi mijin ya mutu ta ci gado. Da zaran namiji ya fahimci manufarta kenan yana iya kauracemata wanda hakan idan ba ayi dace ba aure ya mutu.


Wasu matan kuwa so suke suyi jima'i da namiji su ce masa ya musu ciki domin su tozartashi ko kuma burinsu su yi bidyo ko hoton tsiracinsu domin neman wani biyan bukata. Da zaran namiji ya fahimci haka bayan jima'i Ku na fako guduwa zai yi.


8: Rashin Ni'ima. Wasu matan bawai ni'imar bace kadai basu dashi, duk lokacin da namiji ya sadu dasu sai ya ji ciwo ko sai ya sha wahala. Maza na samun Kansu a irin wannan matan guduwa suke a haduwar farko.


9: Rashin Iya Jima'i: Kama daga wasanni motsa sha'awar, zuwa yanayin kwanciyar na jima'i. Irinsu kukan kissa, rashin iyasu nasa wasu mazan su gudu bayan kwanciyarsu da mace. Idan kuwa matan aurece ba a lokacin da take bukatan jima'i ba zata rika samu.


10: Rashin Kamun Kai: Wasu mazan da zaran sun fahimci basu kadai bane suke zina dake bayan haduwarku na farko to bazaki sake ganinsu ba. Burinsu ya zama su kadai ne suke Jima'i dake.


Sharhi

Yanada kyau 'yan mata su fahimci cewa a dai-dai lokacinda kuke aikata ba dai dai ba kina iya maida ba dai dai din nan ya zama dai dai. Kada yasa zina kawai kika saka a gaba da saurayinki babu tunanin yadda zai bijiro da wasu dabi'u da halayen da zai dawo yaji kin fi da cewa da aure bada iskanci ba. Amma idan kika dauka tunda soyayya irin na zina kukeyi don haka duk rashin mutunci da rashin tarbiyan da ya kama zaki iya yi ko a ina kuma ko a gaban wa, tofa kina cutan kanki ne. Domin na kusa da saurayin zinar taki sune zasu soma kusheki kinaji kina gani ya barki yaje ya auro wata.


Ko da zinace ta haɗa ki da namiji muddin ya sameki da Ɗabi'u masu kyau yana iya sake tunani daga haram zuwa halak. Amma idan ya fahimce ki kwatakwata baki da natsuwar da zai iya maida matarsa, ci gaba da yin zinar dake ne kadai zai saka a gaba kafin ya ingiza ƙeyarki. Don haka ne wasu matan masu dabara maza na zuwa musu da mummunar manufa amma kuma daga bisani sai aga sun ɗaura aure.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post