Tsohuwar jarumar Kannywood Zulai Dalhat ta rasu - Android Pols

Tsohuwar jarumar Kannywood Zulai Dalhat ta rasu
ZULAI DALHAT LILISCO


Tsohuwar jarumar Kannywood Zulai Dalhat wacce aka fi Sani da Zulai Lilisco ta rasu a sakamakon rashin lafiya. Wanda kuma tuni aka yi janaizar ta kamar yadda addini ya tanadar. 


Fitaccen jarumi kuma shugaban Hukumar tace finafinan Kannywood Abba Al-Mustapha ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook kamar haka. 


"INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN 

Allah yayi wa ZULAI DALHAT LILISCO, mata ga dan Uwa kuma Jarumi Shuaibu Lilisco kuma tsohuwar jaruma a masana’artar KANNYWOOD bayan fama da rashin lafiya. Zaayi Jana’izarta yanzu a unguwar TUDUN YOLA. 


Muna Addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata Kurakuranta yasa Aljanna ce makomarta. Idan Tamu Tazo kuma Allah yasa mu çıka da kyau da İmanı. 

R.I.J.F 😭😭😭😭😭"

ZULAI DALHAT LILISCO
ZULAI DALHAT LILISCO

Muna addu'ar Allah ya jikan ta da Rahama ya baiwa iyalanta hakurin jure rashin ta amin.


Related
Previous article
Next article

Ads Atas Artikel

Ads Tengah Artikel 1

Ads Tengah Artikel 2

Ads Bawah Artikel