Takaitaccen Tarihin Hassan Sarkin Dogarai Kano

Takaitaccen Tarihin Hassan Sarkin Dogarai Kano
Takaitaccen Tarihin Hassan Sarkin Dogarai Kano 


Kafin nadin Hassan a matsayin sarkin dogaran fadar Kano, Marigayi Ado ya nada wasu mutane biyu a baya; Dan-Wudil da Adamu, kuma bayan mutuwar Adamu ne aka nada Hassan


Hassan Adamu, da aka fi sani da Hassan sarkin Dogarai, shi ne sarkin Dogarai na uku da marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ya nada a matsayin shugaban dogaran sarki a shekarar 1990.


Jama'a sun kara sanin sa dalilin wakar da marigayi Mamman Shata ya yi masa mai taken Hassan Sarkin Dogarai.


An haifi Hassan Adamu sarkin dogarai a shekara ta alif dari tara da ashirin da biyar (1925).


Kafin nadin Hassan a matsayin sarkin dogaran fadar Kano, Marigayi Ado ya nada wasu mutane biyu a baya; Dan-Wudil da Adamu, kuma bayan mutuwar Adamu ne aka nada Hassan, sannan shi ma bayan mutuwarsa aka nada sarkin Dogarai na yanzu, Danbala.


Saidai sabanin sarkin dogarai Adamu da Dan-Wudil, Hassan ba bafade bane. Asalinsa direba ne dake sana’ar tuka mota kafin daga baya ya zama hadimi ga galadiman Kano, Marigayi Tijjani Hashim, mutumin da ya fara nada shi a matsayin shamakinsa kuma ya zama silar shigar sa cikin fadar Kano.


A shekarar 1990 ne, bayan mutuwar sarkin Dogarai Dan-Wudil, Marigayi Tijjani Hashim ya roki sarkin Kano Ado alfarmar ya nada Hassan a matsayin sarkin Dogarai saboda tsananin biyayyar sa da kuma jarumtar sa, sannan ga soyayya da yake nunawa ga sarkin.


Marigayi Hassan na zaune ne da iyalinsa a unguwar Sagagi, kusa da gidan mahaifiyar Ado Bayero, kafin daga bisani ya koma unguwar gidan sarkin Dogarai dake unguwar Dogarai, daf da gidan sarkin Kano.


Hassan ya yi shura a cikin sarakunan Dogaran Kano saboda karfi da jarumta da kuma tsananin biyayyarsa ga sarkin Kano Ado.


Hassan sarkacecen mutum ne, saboda girma da tsayinsa har kirari ake yi masa da Bishiya.


Wani dan asalin unguwar Dogarai, Ibrahim Mu’azzam Sadauki, da ya san marigayi Hassan, ya shaidawa shafin tarihin kano  cewar, Marigayi Hassan ya fara haduwa ne da shahararren mawakin Hausa, Alh DR Mamman Shata, yayin da yake sana’ar sa ta tuka mota. Bayan Hassan ya zama sarkin Dogarai ne, Shata ya rera masa wakar “Hassan sarkin Dogarai”, wakar da ta kara daukaka sunan Hassan  a fadin Duniya. "Amma Fa A Lura Duk Wasu Abubuwan Da Shata Yake Fada Nasa A Wakarsa Ba Haka Abubuwan Suke Ba Wakace Kawai.


Hassan ya rasu a shekarar 2007. Yanzu haka iyalan Hassan sun koma gidansa dake unguwar Sagagi inda suka cigaba da rayuwa bayan mutuwar mahaifinsu.


Wannan Tarihin Mai Yiwuwa Akwai Abubuwa Da Suka Sauya Bayan Mutuwarsa (UPDATE). Allah Ya Jikansa Da Rahama AMEN


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post