Mene Yake Kawo Yawan Fitar Da Maziyyi

 Mene Yake Kawo Yawan Fitar Da Maziyyi

Yawan fitar maziyyi yana faruwa a sakamakon motsawar sha'awa kamar kallo, shafar mace ko tunani da sauransu. 


Ni namiji ne wanda larurar fitar maziyyi ke damuna. Ina yawan fitar da maziyyi, shin ko menene hukuncin hakan sannan menene hukuncin sallar mutumin da yake fitar da maziyyi. 


Salamun alaikum don Allah ina yawan fitar da maziyyi shin yaya hukuncin sallar mutumin da yake fitar da maziyyi yayin da yake cikin sallah? 


To dan uwa shi maziyyi mafi yawan lokuta yana fitane a sakamakon motsawar sha'awa kamar kallo, shafar mace ko tunani da sauransu. 


Sabida haka idan har kasan cewa fitar maziyyi yana fita ne a sakamakon aikata daya daga cikin abubuwan nan to ya wajaba ka nisanci aikata hakan yayin da za kayi sallar ko kake cikin sallar musamman yin tunanin abinda zai haddasa maka motsawar sha'awar yayinda kake cikin sallah, kenan in dai har fitar maziyyin yana faruwa a dalilin tunanin abinda ke sa fitar maziyyin koda kana cikin sallar to kawai ka yanke sallar kaje ka gusar da najasar sannan ka sake alwala ka sake sabuwar sallah.


Hakanan Idan fitar yawan maziyyi haka kawai yake zubowa amma ba koda yaushe ba, ma'ana a wasu lokutan yake fitowa koda ba tare da motsawar sha'awa ba shima a irin wannan yanayin koda kana cikin sallah kaji fitar maziyyin ya wajaba ka yanke sallar matukar ka samu tabbacin fitar maziyin sabida fitar maziyyi yana karya alwala kamar yadda aka rawaito daga sayyadina Aliyu Allah yakara masa yarda cewa. 


Na kasance mutum mai yawan fitar da maziyyi, sai naji kunyar na tambayi Manzon Allah (SAW) saboda akwai yarsa a wajena (ma'ana saboda ina auren yar sa) sai na umarci Mikdad dan Aswad ya tambayar min Annabi yace masa idan ya fito ka wanke, sai Annabi yace ka sake alwala (@Bukhari da muslim)


Idan kuma yawan fitar maziyyin koda yaushe ne, ma'ana ba sai a lokacin sallah yake zuwa ba koda yaushe kake ganinsa to a irin wannan yanayin hukuncinka zai kasance irin hukuncin me jinin cuta ko matar da take ganin ruwa na fito mata a koda yaushe ko kuma wanda ke da matsalar yoyon fitsari da sauransu. 


Yadda zakayi shine duk lokacin sallah zaka dinga gusar da maziyyin daga jikin tufafınka tare da wanke al'aurar baki dayanta sai ka sanya wani kyalle a al'aurarka kamar dai handkerchief wanda zai hana yawan fitar maziyyin yaduwa a jikinka Bayan nan sai kayi alwala kaje kayi sallarka koda kaji alamun fitar maziyyin kada ka damu da hakan kawai ka cigaba da sallarka har sai ka kammala sallar.


(Don neman karin bayani a duba al'Mughni (1/206)) Wallahu A'alam


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك idan Anga Gyara A Sanar Damu


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post