![]() |
Murja Ibrahim Kunya |
Kotu ta bayar belin shahararriyar yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Nasiru Saminu ya amince da bayar da belin Murja Kunya a kan kudi N500,000 tare da kawo mutane biyu da za su tsaya mata .
kotun ta Kuma umurci hukumar kula da asibitocin jihar Kano da kuma asibitin masu tabin hankali na dawanau da su tabbatar da sallamar Murja kunya bayan ta cika sharuddan belin.