Amfani 9 da ganyen rama ke yi a jikin mutum

Amfani 9 da ganyen rama ke yi a jikin mutum
Amfani 9 da ganyen rama ke yi a jikin mutum

Ganyen rama ana yin fate, dambu, a yi miyar ta zalla ko kuma a hada ta wajen yin miyar taushe, akan kuma dafata a kwada da kuli a ci.


Ganyen rama wato ‘Jute Leaves’ ganye ne da mutane musamman na yankin arewacin Najeriya ke yawan amfani da ita.


Mutanen yankin arewacin Najeriya na yawan amfani da shi, inda yakan zama abincin rana ko na marmari.


Ana yin fate, dambu, a yi miyar ta zalla ko kuma a hada ta wajen yin miyar taushe, akan kuma dafata a kwada da kuli a ci.


Ga irin amfanin da ke tattare da cin ganyen rama:


Amfani 9 da ganyen rama ke yi a jikin mutum

Ga irin amfanin da ke tattare da cin ganyen rama:

1. Ganyen rama na dauke da sinadarin ‘Vitamin A, B, C, D da B-12 dake kara karfin ido, saurin nika abinci a ciki, sa jikin mutum warkewa musamman idan an sami rauni sannan ya na kara jini a jiki.

2. Ana samun sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin kashi.

3. Yana dauke da sinadarin Iron dake kara karfin kashi.

4. Rama na taimakawa wajen hana tsufa da wuri.

5. Yana taimaka wa wajen wanke ciki.

6. Yana rage kiba a jiki da (Tumbi).

7. Yana kawar da bugawar zuciya na farad daya.

8. Yana kawar da ciwon siga.

9. Ganyen rama na magani da kare mutum daga cutar sida ko kuma daji kowane iri.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post