Abubuwa 12 da Mata suka fi so daga namiji fiye da Kudi

Abubuwa 12 da Mata suka fi so daga namiji fiye da Kudi
Abubuwa 12 da Mata suka fi so daga namiji fiye da Kudi


kowa na son kudi kuma yana bukatar su. Bugu da kari, mafi yawan mata na tsammanin ko son wasu abubuwa daga abokan zamansu wanda ya zarce kudi.


Yana da matukar muhimmanci a nemi kudi domin yin rayuwa. Babu shakka kowa na son kudi kuma yana bukatar kudi, amma har ila yau akwai wasu abubuwan bukata fiye da kudi. 


Akwai wasu abubuwa da mata ke so daga abokin tarayya a yayin soyayya ko a zamantakewar aure wanda ya fi kudi.


Gaskiyar ita ce, babu wanda za a saka masa sukari a baki ya tofar ya ce ya fi son ganyen shuwaka, duk da camfi da ake yi cewa mata sun fi son kudi.


A wata mahangar, kowa na son kudi kuma yana bukatar su. Bugu da kari, mafi yawan mata na tsammanin ko son wasu abubuwa daga abokan zamansu wanda ya zarce kudi.


Abubuwa 12 da Mata suka fi so daga namiji fiye da Kudi

1) Mata na son maza da ke nuna musu kauna da kulawa ta gaskiya. Kulawa da sauraran su sune abubuwan da ke hade mace da abokin zamanta. Mata na son namiji da zai saurari abin da suke fada domin koyaushe suna da abin fada.


2) Mata na son maza da ke kiran su akai-akai. Idan ba ka kira mace akai-akai ba, ba za ta iya cewa kana son ta da gaske ba. Kira a gare su alama ce ta gaskiya dake nuna ka damu dasu.


3) Mata na daraja maza da ke nuna aminci a gare su. Ga mafi yawan mata, rashin aminci a dangantaka abu ne da ba za a iya yarda da shi ba. Da zarar ka yi rashin aminci, ba ka cancanci zama miji ba.


4) Mata na son maza masu sassaucin ra’ayi da 'yanci. Mata basa son namiji mai karfin ra'ayi kan abu, wanda idan yana ra'ayi akan abu baya sauyawa. 


5) Suna son maza da ke matukar daraja iyayensu. Duk Mace na son saurayi ko mijinta yana girmama iyayenta tamkar Iyayensa. Wannan yana kara dankon soyayya a tsakanin mace da namiji. 


6) Mata na son namiji da ke girmama mace da mutunta ta. wanda yake shirye ya tsaya mata har a bainar jama’a. Duk Mace na alfahari da fatan samun miji mai irin wannan halayyar. 


7) Mata na son namiji da ya iya soyayya da kauna. Wanda zai sa ta ji tana bukatar sa kuma tana kaunar sa


8) Mata na son maza da za su iya sa mace dariya akai-akai. Maza masu wasan barkwanci da kalamai irin wanda ke sa dariya da nishadi. 


9) Mata na son namiji da ba zai zarge ta da laifukan da ta aikata a baya ba. Wasu Mazan idan mace tai musu laifi basa mantawa, kuma za su dinga yawan yi mata gori akai. Mace bata son irin wannan namijin. 


10) Mata na son maza da ke shirye su tsaya musu da taimaka musu a cikin dukkan ayyukanta. Misali ayyukan gida da kuma sana'a da take yi, tana son ta ga an tallafa mata. 


11) Mata na son namiji da ke inganta su a matsayin mutane da abokan tarayya. Namiji wanda a ko ina zai iya nunawa mace ita matarsa ce abar Kaunarsa. 


12) Mata na son namiji da ke shirye ya sanar da duniya cewa ya gano kasusuwan da ya dade yana nema. Ma'ana yana alfahari da samun matarsa wacce yake burin samu. 


Wannan sune abubuwa 12 da mata suka fi so daga namiji fiye da kudi, ba kamar yadda wasu ke tunanin cewa su mata kawai kudi suka fi bukata, sai dai ba haka abin yake ba. Ita mace tana son kulawa, nuna soyayya, daukar dawainiyarta da kare ta. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post